Fim din ‘Spiderman-2’ ya mamaye kasuwar China
Sabon fim din ‘Spiderman-2’ ya mamaye kasuwannin kasar China, inda a halin yanzu ya yi cinikin Dala miliyan 45.9, wanda haka ya sanya ya mamaye kashi 60 cikin dari na kasuwar fina-finan da aka fitar a wannan tsakanin, kwanaki shida kacal da fitar da shi kasuwa.Duk da cewa har yanzu kasuwar fim din ba ta […]

Sabon fim din ‘Spiderman-2’ ya mamaye kasuwannin kasar China, inda a halin yanzu ya yi cinikin Dala miliyan 45.9, wanda haka ya sanya ya mamaye kashi 60 cikin dari na kasuwar fina-finan da aka fitar a wannan tsakanin, kwanaki shida kacal da fitar da shi kasuwa.
Duk da cewa har yanzu kasuwar fim din ba ta kamo cinikin fim din ‘Captain America: The Winter Soldier’ ba, wanda ya samar da cinikin sama da Yuan miliyan 700, duk da haka yana kan hanyar samar da cinikin ban mamaki; kamar yadda kafar watsa labarai ta Dinhua ta ruwaito.
Fim din na ‘Spiderman,’ wanda kamfanin Sony ke mallakarsa, shi ne fim irinsa na farko da aka gabatar a kasuwannin fim na kasar China.