Fina-finan Bogi: ‘Yan fim sun yi zanga-zanga a Legas

Jaruman fim daga Kudancin Najeriya (Nollywood) da furodusoshi da kuma dillalan fim sun gudanar da zanga-zangar lumana don yin Allah-wadai da mamayar da fina-finan bogi suka yi wa a kasuwanni a Jihar Legas. ’Yan fim din sun taru a unguwar Ikeja inda suka dunguma zuwa gidan gwamnatin jihar dauke da kwalaye da kyallayen da ke […]

Fina-finan Bogi: ‘Yan fim sun yi zanga-zanga a Legas
Fina-finan Bogi: ‘Yan fim sun yi zanga-zanga a Legas

Jaruman fim daga Kudancin Najeriya (Nollywood) da furodusoshi da kuma dillalan fim sun gudanar da zanga-zangar lumana don yin Allah-wadai da mamayar da fina-finan bogi suka yi wa a kasuwanni a Jihar Legas.

’Yan fim din sun taru a unguwar Ikeja inda suka dunguma zuwa gidan gwamnatin jihar dauke da kwalaye da kyallayen da ke dauke da sakonnin da ke neman gwamnati ta dakatar da masu sayar da fim din bogi a Legas.
’Yan fim din sun yi ta rera wakoki tare da yin kade-kade da raye-raye da bushe-bushe, a harabar gidan gwamnatin jihar, suna jiran Gwamna Fashola ya yi musu jawabi.
Kafin gwamna ya fara jawabi sai da jagoran masu zanga-zangar mai suna Tunde Kelani, ya yi jawabi inda ya shaida wa gwamnan cewa sun fito ne don su shaida wa duniya da gwamnati halin da suka shiga sakamakon masu sayar da fim din bogi.
Kelani ya ce masu sayar da fim din bogi na cin karensu ba babbaka kuma suna ci da guminsu ba tare da an dauki mataki a kansu ba.
Ya bayyana cewa ta kai idan suka fitar da fim ba sa samun riba saboda irin yadda masu buga fim din bogi ke satar fasaharsu su sayar ba tare da wata matsala ba.
A nasa jawabin, Gwamna Babatunde Raji Fashola, ya yaba wa kokarinsu na neman hakkinsu ta hanyar da ta dace.
Ya nemi su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda a duk loacin da za su nemi duk wani hakki nasu.
Ya yi musu alkawarin cewa gwamnatin za ta hada kai da hukumomi domin daukar matakan da suka dace.