Fina-finan Duniya: Mahimman Al’amura a 2013
A 2013, a duniyar fina-finan Ingilishi daga Najeriya da Amurka da Indiya, an samu tumbatsar ingantattun fina-finai, kamar kuma yadda ’yan wasa maza da mata suka samu daukaka da dukiya saboda namijin kokarinsu. Ga wasu daga cikin irin wadannan al’amura: Najeriya (Nollywood) a 2013Fina-finan Ingilishi a Najeriya sun samu canjin yanayi a 2013, musamman ma […]

A 2013, a duniyar fina-finan Ingilishi daga Najeriya da Amurka da Indiya, an samu tumbatsar ingantattun fina-finai, kamar kuma yadda ’yan wasa maza da mata suka samu daukaka da dukiya saboda namijin kokarinsu. Ga wasu daga cikin irin wadannan al’amura:
Najeriya (Nollywood) a 2013
Fina-finan Ingilishi a Najeriya sun samu canjin yanayi a 2013, musamman ma saboda ana amfani da ingantattun na’urori da kwararrun ma’aikata da fitattun ’yan wasa wajen shirya su. Ga fina-finai goma da suka fi shahara a Najeriya (Nollywood): 1-Fim din ‘A Mile From Home’ wanda Eric Aghimien ya shirya kuma ya ba da ummurni. 2-Fim din ‘Phone Swap’ wanda Kunle Afolayan ya shirya. 3-Fim din ‘Tango with me’ wanda Mahmood Ali-Balogun ya shirya. 4-Fim din ‘On Bended Knees’ wanda Chioma Chikwuka-Akpotha ta shirya. 5-Fim din barkwanci na ‘House of Gold’ wanda Ybonne Nelson ta shirya. 6-Fim din ‘Weekend Getaway’ wanda na soyayya ne da Monalisa Chinda da Ino Ehiagwina suka shirya. 7-Fim din ‘Playing Safe’ an shirya shi a Legas da Dubai da Ghana da Landan kuma kamfanin Elbis Chuks Production ya shirya shi. 8-Fim din ‘Shameful Deceit’ Theodora Ibekwe ne ya shirya shi. 9-Fim din ‘Torn’ Moses Inwang ne ya shirya shi kuma ya ba da umurni. 10-Fim din ‘Murder at Prime Suites’ Jumafor Ajogwu ne ya shirya shi.
A fagen ’yan wasa kuwa, ga jerin wadanda suka fi yin fice a 2013: Jim Iyke, Odunlade Adekola, Ramsey Nouah, Richard Mofe Damijo, Bolaji Amusan, Ibu John Okafor, Nkem Owoh (Osufia), Osita Iheme (Pawpaw) da Chinedu Ikedieze (Aki). Sauran sun hada da Emeka Ike, Nonso Diobi, Mike Ezuruonye da Desmond Elliot.
A mata kuwa, wadannan su ne a sahun gaba a 2013: Funke Akindele, Omotola Jalade Ekeinde, Kate Henshaw, Genebiebe Nnaji, Mercy Johnson, Stephanie Okere Linus, Ini Edo, Monalisa Chinda da Uche Jombo. Sauran sun hada da Patience Ozokwor, Omoni Oboli, Tonto Dike da kuma Stella Damasus.
Amurka (Hollywood) a 2013
A harkar fim a Amurka a 2013 kuwa, an samu shahararru kuma fitattun fina-finai kamar haka: 1-Fim din ‘Iron Man 3.’ 2-Fim din ‘The Hunger Games: Catching Fire.’ 3-Fim din ‘The Hobbit: The Desolation of Smaug’ 4-Fim din ‘Thor: The Dark World.’ 5-Fast & Furious 6.’ 6-Fim din ‘Pacific Rim.’ 7-Fim din ‘Man of Steel.’ 8-Fim din ‘Grabity’ 9-Fim din ‘Now You See Me.’ 10-Fim din ‘Despicable Me 2.’
Haka kuma, shahararrun ’yan wasa mata da suka taka muhimmiyar rawa a 2013, sun hada da: Jessica Alba, Jennifer Aniston, Cameron Diaz, Emma-Stone, Mila-Kunis da Scarlett-Johansson. Sauran sun hada da Julia Roberts, Marion-Cotillard, Charlize-Theron da kuma Angelina-Jolie.
Indiya (Bollywood) a 2013
Kamar sauran sassan duniya, harkokin fim a Indiya sun samu ci gaba a 2013 kuma ga wasu fitattun fina-finai da suka yi tashe a shekarar: 1-Fim din ‘bishwaroopam’ wanda Kamal Hassan ya ba da Umurni. 2-Fim din ‘Special 26’ wanda Akshay Kumar ya jagoranci sauran ’yan wasa. 3-Fim din ‘Kai po che’ wanda Abhishek Kapoor ya ba da umurni. 4-Fim din ‘The Attacks of 26/11’ wanda aka shirya daga labarin abin da ya faru na gaskiya. 5-Fim din ‘Raanjhanaa. 6-Fim din ‘Lootera.’ 7-Fim din ‘Bhaag Milkha Bhaag.’ 8-Fim din ‘Ship of Theseus.’ 9-Fim din ‘B.A. Pass.’ 10-Fim din ‘Prague’ wanda Ashish R. Shukla ya ba da umurni kuma Chandan Roy Sanyal ya jagoranci ’yan wasa.
Ta bangaren ’yan wasa kuwa, fitattun da suka taka muhimmiyar rawa a 2013 sun hada da Shah Rukh Khan, Ranbir Kapoor, Hrithik Roshan da Salman Khan. Sauran sun hada da Farhan Akhtar, Ranbeer Singh da John Abraham da Akshay Kumar da Aamir Khan da kuma Aditya Roy Kapur.
A mata kuwa sunayen da suka fito sarari a 2013 sun hada da bidya Balan, Sonakshi Sinha, Deepika Padukone da Kareena Kapoor da kuma Katrina Kaif.