Fina-finan ‘Hausa-Indiya’ sun yi wa Kannywood shaken mutuwa – AS Mai kwai

Alhaji Abubakar AS Mai kwai shi ne shugaban kamfanin shirya fina-finai na Mai kwai Mobies, ya shafe fiye da shekara 15 a Kannywood, a kwanakin baya ya kawo wa Aminiya ziyara a ofishinta da ke Abuja, wakilin Aminiya ya tattauna da shi kan batutuwan da suka shafi Kannywood musamman al’amuran da suka shafi satar fasaha […]

Fina-finan ‘Hausa-Indiya’ sun yi wa Kannywood shaken mutuwa – AS Mai kwai
Fina-finan ‘Hausa-Indiya’ sun yi wa Kannywood shaken mutuwa – AS Mai kwai

Alhaji Abubakar AS Mai kwai shi ne shugaban kamfanin shirya fina-finai na Mai kwai Mobies, ya shafe fiye da shekara 15 a Kannywood, a kwanakin baya ya kawo wa Aminiya ziyara a ofishinta da ke Abuja, wakilin Aminiya ya tattauna da shi kan batutuwan da suka shafi Kannywood musamman al’amuran da suka shafi satar fasaha da kuma fina-finan Hausa-Indiya

Za mu fara da jin takaitaccen tarihinka?

Assalamu alaikum, sunana Abubakar A S Mai kwai, wanda yake jagorantar kamfanin shirya fina-finan Hausa mai suna Mai kwai Mobies da ke Jihar Kano. An haife a Unguwar dandago Sabon Titi da ke karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano a shekarar 1983. Na yi ilimin firamare dandago Primary School, sannan na yi makarantar sakandare a Gwale, daga nan na ci gaba da karatu har Allah Ya kawo ni masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood).
Me ya ja hankalinka har ka fara shirya fina-finai?
Idan har mutum yana so ya isar da sako to dole sai ya yi amfani da kafafen yada labarai, a fahimta idan gwamnati ko malamai ko masarautu da sauransu suna son isar da wani sako, to dole sai sun yi amfani da kafar yada labarai, abin da ya ja hankalina shi ne, na fahimci za a iya amfani da Kannywood wajen isar da dukkan sakon da mutum yake son isarwa. Ma’ana Kannywood hanya ce ta kai sako. Duk wani abu da kake so ka nuna wa al’umma amfaninsa ko illarsa, to za ka iya isar da shi ta Kannywood. Akwai matsaloli da ake fuskanta ta bangaren tarbiyya da kuma abin da ya shafi rayuwar aure da sauransu. Matsalolin da ake samu a bangaren auratayya na damu na, hakan ya sa na shiga harkar fim don in isar da sakon gyara a bangaren rayuwar aure, shi ya sa yawancin fina-finaina sun shafi ma’aurata misalinsu: ‘Malika’ da ‘Matan Gida’ da ‘Zawarawa’ da sauransu.
Ko me ya sa ka sanya wa kamfaninka sunan ‘Mai kwai Mobies’?
Ina da kamfanoni biyu a Kannywood, ba da kamfanin Mai kwai Mobies na fara ba, sunan kamfanina na farko TMA Production, wanda na yi amfani da shi akalla tsawon shekara takwas ko goma, daga baya sai na bude kamfanin Mai kwai Mobies, wanda a yanzu na fi shirya fina-finai da shi. Sana’ar sayar da kwai ita ce sana’ar da na fara, kuma jama’a da yawa a kanta suka san ni kafin in shiga harkar fim. Bayan na shigo Kannywood sai jama’a suke kira na da Abubakar Mai kwai, hakan ya sa bayan na bude kamfanin TMA Production, sai na bude Mai kwai Mobies.
Ka dade a Kannywood, kuna daya daga cikin wadanda suka raine ta har ta tsaya da kafafunta, kawo yanzu wadansu matsaloli kake fuskanta?
Mun fuskanci kalubale da dama, amma a yanzu muna da babban tashin hankali a gare mu, da shi muke kwana, kuma da shi muke tashi, wato ya kamata a ce jami’an gwamnati da masu kudi su kalle mu da idon rahama, saboda Kannywood ta kusa zama tarihi, akalla masana’antar ta samar wa mutane sama da dubu 300 aikin yi, amma a yanzu wadansu mutane sun buwaye mu, domin suna fassara fina-finan Indiya zuwa Hausa, abin takaicin shi ne, mu da Indiya din nan al’adunmu ba daya ba ne, suna yin badala da sauran maganganun marasa kan gado a fina-finansu, amma wadannan mutanen suna ta yada su, mutum da iyalinsa ko ’yan uwansa ba za su iya kallon fim din a wuri daya ba. Abin ban haushin shi ne, jama’a sun karkata ga kallon wadannan fina-finan. Wadannan fina-finan suna neman kashe fina-finanmu. Wani abu kuma shi ne, jama’ar gari suna danganta mu da wadannan fina-finan Hausa-Indiya din. Maganganun da ake yi a fina-finan Hausa-Indiya addinin Musulunci da na Kirista ba su yarda da su ba.
Matsala ta biyu ita ce, batun satar fasaha da ya yi wa Kannywood shaken mutuwa, mutum zai sha wahala ya sayi labari, ya dauki labarin ya bayar don neman shawara (consultancy), bayan an gama, ya tara ma’aikata a dauki fim din, daga na ya biya gwamnatin jiha da ta tarayya. Kowane fim sai ya biya gwamnatin Tarayya dubu 50, gwamnatin jiha kuma dubu goma da dari biyar, idan ya gama, sai ya biya kudin hakkin mallaka a wurin Hukumar Hakkin Mallaka ta Najeriya, daga nan watakila ya dauki shekara yana tallar fim din, duk da kashe kudin da ya yi, ranar da ya fito da fim din sai ka samu wani mutum ya sayi faifan Naira 15 ya kwafe shi, sannan ya rika sayarwa, a karshe a dawo da mai fim nasa domin babu ciniki, mutane sun fi sayan na mai satar fasaha, saboda ya fi arha, a karshe bayan mai fim ya yi lissafi ya gane an shiga uwar kudi, maimakon a samu riba. Wannan al’amari yana damun mu. Don haka muna rokon gwamnati ta taimaka mana don a kawo karshen satar fasaha a kasar nan.
Na taba jin wani mai sharhi kan fina-finan Hausa yana cewa dalilin da ya sa fina-finan Hausa-Indiya suke neman nakasa fina-finan Kannywood shi ne, da yawa daga cikin masu shirya fina-finan Hausa labaran fina-finan Indiya suke juyawa, sannan ba sa yin fim kan doron addini da kuma al’adar Hausawa, ko me za ka je kan hakan?
Wannan mai sharhin ya kamata ya sake nazari a kan sharhinsa, abin da ya sa na ce haka kuwa shi ne, idan har yana kallon fina-finan Indiya da kuma na Hausa, to zai tabbatar al’ada da addininmu ya bambanta da na Indiya, saboda addininmu da al’adarmu ba ta yarda da batsa ba, kuma wadannan fina-finan da ake fassarawa suna cike da batsa, kuma shi kansa ba zai iya kalla da iyalinsa ba, sannan yawanci fina-finan Indiya za a ga suna dauke da dambace-dambace da kuma fadace-fadace, amma a namu babu haka, wadannan fina-finan da ake fassarawa kuwa suna dauke da fadece-fadace ne, za ka ga ana tashi sama, ko su ma Indiya din hakan ai ba al’adarsu ba ce. Don haka batun a ce mun sake al’adarmu ce shi ya sa jama’a suka koma kallon Hausa-Indiya, sai in ce ya kamata mai sharhin ya sake dubawa. Har yau ba za ka kalli fim din Hausa daga farko har karshe ba ka ji an ce ‘La’ilaha Illallahu Muhammadur Rasulillahi’ ba. Idan kuwa haka ne ka ga akwai abin da ya shafi addini, duk da yake addinin Musulunci ya wuce a yi tallansa, addini ne na Allah kuma Ya yi alkawarin tsare abinSa.
Wane buri kake so ka cim ma a Kannywood?
Ka san dan Adam ba a raba shi da buri, kuma kullum burinmu a wannan masana’anta mu rika karbar gyararraki, har yanzu mu masu tasowa ne, burinmu komai ya daidaita har Kannywood ta rika gogayya da Hollywood. Burina shi ne, Allah Ya dora mu a kan tafarki madaidaici. Sannan babban burina a amfana da wadannan fina-finan da muke yi ko da bayan ranmu ne. Ina da kuma burin Kannywood ta bunkasa.
Shawararka ga masu kallo?
Ina so masu kallo su rika yi mana uzuri, su fahimta mu ajizai ne, ’yan Adam ne kamar kowa, su fahimta kofofinmu na karbar gyara a bude suke. Ina kira ga ’yan kallo su daina sayen fina-finai daga wurin masu satar fasaha, su daina sayen fina-finan Hausa-Indiya, idan ba su daina ba, to gaba ba za mu iya ci gaba da yin fina-finai ba.