Fina-finan Hausa: Muhimman al’amura 13 da suka faru a 2013

A 2013, a duniyar fina-finan Ingilishi daga Najeriya da Amurka da Indiya, an samu tumbatsar ingantattun fina-finai, kamar kuma yadda ’yan wasa maza da mata suka samu daukaka da dukiya saboda namijin kokarinsu. Ga wasu daga cikin irin wadannan al’amura: 1-Mutuwar Mawakin Hausa Ahmadu DokaA ranar Litinin, 7 ga watan Janairun 2013 ce Allah Ya […]

Fina-finan Hausa: Muhimman al’amura 13 da suka faru a 2013

Bangon fim din Matan Gida, daya daga fina-finan da suka yi armashi a 2013A 2013, a duniyar fina-finan Ingilishi daga Najeriya da Amurka da Indiya, an samu tumbatsar ingantattun fina-finai, kamar kuma yadda ’yan wasa maza da mata suka samu daukaka da dukiya saboda namijin kokarinsu. Ga wasu daga cikin irin wadannan al’amura:

1-Mutuwar Mawakin Hausa Ahmadu Doka
A ranar Litinin, 7 ga watan Janairun 2013 ce Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa, Alhaji Ahmadu Doka rasuwa. Ya mutu yana da shekaru 82 a duniya. Kafin rasuwarsa, shi ne Dagacin Abakwa da ke cikin garin Kaduna. Ya rasu ya bar mata da ’ya’ya 36. An kuma yi jana’izarsa ne a makabartar da ke kan titin Bashama, Tudun Wada, Kaduna.

2-Bikin Makon Mawakan Hausa
A cikin watan Janairun 2013 ne aka gudanar da Bikin Makon Mawakan Hausa na farko a Kano. Kamfanin mawakin Hausa, Aminu ALA ne ya shirya gangamin. A yayin bikin ne kuma aka karrama wasu mawaka da marubuta su bakwai, wadanda muhimman mutane daban-daban suka mika wa kyaututtuka. Cikin wadanda aka karrama sun hada da Ado Ahmad Gidan Dabino.
Bikin dai ya samu halartar shahararrun mutane da mawakan Hausa da kuma wasu shahararrun ’yan fim. Manyan mutanen sun hada da Alhaji Aminu Ado Bayero da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, da sauransu. Cikin ’yan fim kuwa, sun hada da Isa Bello Ja da Saratu Gidado (Daso) da Hadiza Gabon da Nura Hussaini da Malam Haruna. Sai kuma mawakan da suka hada da Rabi’u Dalle da Aminu ALA da Auwal Yobo da Adamu Hassan Nagudu da Misbahu M. Ahmad da Mudassiru Kasim da Nura M. Inuwa da Naziru Abdullahi Magoga (Indiya) da Sadik Zazzabi. Sauran sun hada da Alkasim D. Bature da Fati Nijar da Baba Chinedu da Tijjani Gandu da Sagir Lalayyo, da dai sauransu.

Gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, yana daga kambin karramawar MTN3-Bikin karrama ’yan fim na MTN
A cikin watan Nuwamba, 2013 Kamfanin Sadarwa na MTN ya shirya gagarumin bikin karrama ’yan fim din Hausa a Kano. Bikin ya gudana cikin armashi, inda har Gwamnoni biyu, na Kano da Kaduna suka halarta. A wajen bkin, an karrama ’yan fim da kyaututtuka iri daban-daban. Shi ne biki irinsa na farko da kamfanin sadarwa ya taba shirya wa ’yan fim din Hausa. Bikin zai ci gaba da gudana a duk shekara, kamar yadda suka yi alkawari.

4-Gwamnoni sun fara na’am da fina-finan Hausa
A cikin 2013, harkar fim din Hausa ta samu ci gaba, musamman ganin yadda wasu gwamnoni suka fara yin na’am da ita. Misali, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso ya rungumi ’yan fim, ya karrama su. Ya shirya masu bita da kwasa-kwasai, kamar kuma yadda ya yi alkawarin gina masu kwalejin koyar da ilimin sana’ar tasu. Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, shi ma yana halartar tarukan ’yan fim, kamar yadda kuma yake tallafa masu. Haka shi ma Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, ya yi na’am da su, inda har ma ya dauki nauyi aka shirya fim din Hausa na tarihinsa.

5-Ali Nuhu ya sake zama fitaccen jarumi
Kamfanin MTN sun zabi Ali Nuhu a matsayin jarumin-jarumai na 2013. Kodayake ba wannan ne karon farko da ya samu kyautar karramawa ba, wannan ita ce karramawa ta farko da ya samu irinta, kasancewar MTN ne na farko da suka kirkiro wannan bikin, cikin kamfanonin sadarwa da ke harkokinsu a Najeriya.

6-Wasu muhimman fina-finai a 2013
Wasu muhimman fina-finai da suka samu amsuwa a 2013 sun hada da ‘Matan Gida’ da ‘Ahlul Kitab’ da ‘Fulani’ da ‘Basaja’ da ‘Karan Bana’ da ‘Rayuwa Bayan Mutuwa,’ da sauransu.
A fina-finan barkwanciu kuwa, akwai ‘karangiya’ da ‘Oga Abuja’ da ‘Kicimilli’ da ‘kara’i’ da dai sauransu.

7-Wasu Fitattun ’yan wasa a 2013
A 2013, an samu ’yan wasa maza da mata da suka yi kokari sosai a sana’arsu, wanda haka ya sanya har suka samu fice. Irin wadannan ’yan wasa kuwa sun hada da Ali Nuhu da Sani Musa Danja da Adam A. Zango da Zaharaddin Sani da Abba El-Mustapha da Abbas Sadik da Abubakar Baballe Hayatu. Sauran sun hada da Abubakar dan Auta da Al-Amin Buhari da Aminu Baba Ari da Daushe da Rabilu Musa dan Ibro. Akwai kuma Rabi’u Rikadawa da Sadik Sani Sadik da sauransu. A mata kuwa, akwai Nafisa Abdullahi da A’isha dankano da Asamau Sani da Fati Ladan da Fati Macijiya da Hadiza Gabon da Jamila Umar. Akwai kuma Ladidi Tubless da Maryam Booth da Maryam Gidado (Babban Yaro) da Maryam Malika da sauransu.

8-Zaharaddin da Ladi sun samu karramawa
Zahraddin Sani da Ladi Mutu-Ka-Raba sun shiga tarihi a 2013, inda suka samu karramawa daga MTN. A yayin da shi Zaharaddin ya samu kyautar fitaccen mai tallafa wa jarumin jarumai maza saboda kokarinsa a fim din ‘Fulani,’ ita Ladi ta samu tata kyautar ce irin wannan a mata saboda kokarinta cikin fm din ‘Kicimilli.’

9-Aminu Saira ya zama fitaccen darakta
A fagen ba da umurni a fina-finan Hausa, Aminu Saira ne ya yi zarra a 2013. MTN sun karrama shi da kambin darakta mafi shahara, a yayin gudanar da gagarumin bikin da suka shirya a Kano a cikin shekarar.

10-An karrama tsofaffin ’yan wasa
A 2013, kamfanin MTN ya kula da tsofaffin ’yan fim na dauri, inda aka ba su kyautar gamsuwa da himmarsu a sana’ar fim duk tsawon rayuwarsu. Wadannan ’yan wasa kuwa sun hada da Sani Mu’azu da Ibrahim Mandawari da Audu Kano (karkuzu) da Samanja da Hamisu Iyantama.

11-Nafisa Abdullahi ta ciri tuta
Kamfanin MTN sun zabi Nafisa Abdullahi a matsayin jarumar-jarumai ta 2013. Wannan ita ce karramawa ta farko da ta samu irinta daga MTN, domin su ne na farko da suka kirkiro wannan bikin, cikin kamfanonin sadarwa da ke harkokinsu a Najeriya.

12-Rasuwar Fadar Bege
A cikin watan Oktoban 2013 ne shahararren mawakin begen Manzon Allah (SAW), Umar Abdul’aziz, wanda aka fi sani da lakanin ‘Fadar Bege’ ya rasu. Mutuwarsa kuwa ta girgiza al’umma da dama. Allah Ya jikansa da gafara, amin.

13-An karrama Zango da Nafisa a Ghana
A ranar 17 ga Yuni, 2013, Sarkin Muslmin birnin Kumasi da ke Ghana, Alhaji Umar Faruk Sa’id, tare da hadin gwiwar kamfanin shirya fina-finai na Yahaleed Production suka karrama Adam A. Zango da kuma Nafisa Abdullahi saboda yabawa da irin fina-finansu.