Fina-finan Musulunci: Rayuwa da ayyukan marigayi Mustapha Akkad

Ga duk wanda ya kalli fina-finan Lion of the Desert da kuma The Message, babu shakka ya san duk wanda ya shirya wadannan fina-finai ya yi wa Musulunci hidima. Wane ne to ya shirya kuma ya ba da umurni a wadannan fitattun fina-finai na Musulunci da wasu irinsu? Marigayi Mustapha Akkad, shi ne wannan gwarzo […]

Fina-finan Musulunci: Rayuwa da ayyukan marigayi Mustapha Akkad
Fina-finan Musulunci: Rayuwa da ayyukan marigayi Mustapha Akkad

Ga duk wanda ya kalli fina-finan Lion of the Desert da kuma The Message, babu shakka ya san duk wanda ya shirya wadannan fina-finai ya yi wa Musulunci hidima. Wane ne to ya shirya kuma ya ba da umurni a wadannan fitattun fina-finai na Musulunci da wasu irinsu? Marigayi Mustapha Akkad, shi ne wannan gwarzo daya tankan da goma da ya samu wannan martaba. Shi ne zakakurin da ya baje kolin fasaha da kishin Musulunci, ya shirya wadannan fina-finai, kuma ya ba da umurni a cikinsu. 

Wane ne Mustapha Akkad? Shi dai wannan dan taliki, an haife shi ne a garin Aleppo na kasar Syria, a ranar daya ga watan Yuli na shekarar 1930. Tun yana yaro matashi ya fara sha’awar fina-finai, wanda dalili ke nan tun yana dan shekara 19 ya fara yunkurin tafiya kasar Amurka, ba don komai ba sai domin ya cika burinsa na zama mai shirya fina-finai.
A lokacin da ya gaya wa mahaifinsa niyyarsa ta zuwa Amurka, sai ya ba shi kudin jirgi da kwafin Alkur’ani. Mahaifin nasa ya shaida masa cewa iya abin da zai iya ba shi ke nan. Shi kuwa Mustapha, yana isa Amurka sai ya samu gurbin karatu a Jami’ar Carlifonia da ke Los Angeles, inda a nan ya karanta Ilimin Wasannin Kwaikwayo, daga bisani kuma ya ci gaba da karatunsa, ya samu digiri na biyu.
Bayan ya samu isasshe kuma gamsasshen ilimi a harkar shirya fina-finai, sai ya fara aiki da kamfanin fina-finai na TB, inda ya shirya fina-finan tarihin wasu kabilu na kasar Amurka da kuma yadda rayuwarsu ta kasance kasar. Wannan fim da ya shirya, shi ya koya masa wani babban darasi a rayuwarsa, domin kuwa wani kamfani mai suna NBC ya nemi ya dauke shi aiki, da alkawarin zai ba shi ingantaccen albashi amma da sharadin ba zai rika sanya sunansa ga duk wani fim da ya shirya ba.
Darasin da ya samu daga wannan bayani kuwa shi ne, mai shirya fim yakan samu suna da shahara, wadanda abin bukata ke nan a sana’ar da suka fi kudi muhimmanci. Kan haka ne ya jajirce, a shekarar 1976 ya shirya gagarumin fim dinsa, wanda duniya ta jinjina masa. Wannan fim kuwa, mai suna The Message, ya shirya shi ne bisa la’akari da tarihin Manzon Allah, Muhammad (SAW), wanda kuma ya shafi tarihin Musulunci gaba daya. Shi ya shirya fim din kuma ya ba da umurni, inda ya fito da Anthony kuinn da Irene Papas a matsayin taurarin da suka jagoranci fim din.
Duk da cewa fim din nan na The Message ya shiryu kuma ya amsu ga al’umma, musamman ma Musulmin duniya, masana’antar fina-finan Amurka ba ta yi na’am da shi ba, ba don komai ba sai saboda wai bai nuna hoton Manzon Allah (SAW) a cikinsa ba. A cewar su, ai Muhammad (SAW) shi ne jigon tarihin Musulunci, wanda aka dora fim din a kansa, don haka a ganin su, babu dalilin da zai hana a nuna tauraron da zai wakilce shi. Shi kuwa Furodusa Mustapha Akkad, yana da kwakkwarar hujjar da ta hana shi yin haka, watau Shari’ar Musulunci.
Ganin irin yadda Mustapha Akkad ya fara shahara a fagen shirya ingantattun fina-finai, wani gwani a wannan fage, John Carpenter ya kawo masa wani daftarin tsararren labarin fim din Halloween, a shekarar 1978. Nan da nan kuwa ya amince ya zama furodusan fim din, a yayin da shi kuma John ya zama mai ba da umurni. Bayan fitowar fim din kuwa, ya samu amsuwa sosai a kasuwa, kasancewar gwanaye biyu ne suka hadu suka samar da shi.
A 1981 kuwa, sai Mustapha ya kuduri aniyar ci gaba da ba da umurni a fim, inda ya fito da ingantaccen fim dinsa na Lion of the Desert, fim din da ke bayyana irin gwagwarmayar da al’ummar Libya suka fafata da Turawan mulkin mallaka na kasar Italiya. A fim din, Anthony kuinn ne ya kasance tauraro, inda ya fito a matsayin Umar Al-Mukhtar. An samu tabbacin cewa Shugaban kasar Libya, marigayi Mu’ammar Gaddafi ne ya dauki nauyin shirya fim din. Wannan fim din shi ma ya shahara sosai a duniya, musamman ma duniyar Musulmi kuma shi ne fim na karshe da Akkad ya ba da umurni a cikinsa.
Bayan wannan fim na Umar Mukhtar, sai ya bar aikin darakta, ya ci gaba da shirya fina-finansa na tarihin gwarazan Musulunci. A shekarar 1995 ne ya kuduri aniyar shirya fim game da rayuwar shahararren gwarzon Musuluncin nan, Saladin. Abin bakin ciki shi ne, bai samu wannan dama ba, domin kuwa an gaza samar da isassun kudi ko kuma wanda zai dauki nauyin shirya shi. Sai da ya kwashe sama da shekara goma yana neman wanda zai dauki nauyin fim din nan, amma bai samu ba. Haka labarin fim din ya ci gaba da zama a teburinsa a yashe.
Ta fuskar iyali kuwa, Mustapha Akkad ya auri Patricia Akkad, wacce suka haifi ’ya’ya biyu tare da ita, kafin su rabu. Sunan ’ya’yan nasa Malek Akkad da Rima Akkad Monla. Ya sake yin wani auren, inda ya sake haihuwar wasu ’ya’yan guda biyu, Tarek Akkad da Zeido Akkad.
Mustapha Akkad dai ya rasu ne a ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2005, a sanadiyyar wani bom da ya tashi a wani otel din da yake zaune a garin Amman na kasar Jordan. An yi ittifakin cewa ’yan kwatar ’yancin Musulunci ne suka saka wannan bom, wanda ya yi sanadiyyar halaka shi tare da diyarsa daya.
Kamar yadda wadanda suka san shi suka tabbatar, shi mutum ne mai tsananin kishin Musulunci. Dalili ke nan ma ya kasance mai himma da kokarin shirya fina-finan da suka shafi tarihin addinin. Kamar yadda abin ya kasance, duk da cewa shi kwararren mai shirya labaran fina-finai ne, amma ya ki shirya kowane irin fim sai na tarihin Musulunci. Babban burinsa a duniya, kamar yadda ya kudurta, shi ne ya bayyyana tsagwaron ainahin labarin Musulunci ga Turawan Yamma, ba kamar yadda ake gurbata tarihin addinin ba.
Wani abin takaici ga duniyar Musulmi shi ne, yadda rayuwar Mustapha Akkad ta salwanta. Domin kuwa, shi ne gwarzon da ya ba da iliminsa da hikimarsa da lokacinsa wajen yi wa Musulunci hidima ta fannin sana’arsa, amma sai ga shi kuma wasu da suke daukar kansu a matsayin ’yan jihadin Musulunci, sun yi sanadiyyar kashe shi da bom. Za a iya cewa, tun bayan rasuwarsa a 2005, shekaru shida da suka gabata, har yanzu ba a samu wani kamarsa ba a duniyar Musulunci, ta fuskar shirya fina-finai irin nasa.
Ko me ya ba shi kwarin gwiwar shirya fim din The Message? Tambayar da aka taba yi masa ke nan a shekarar 1977, inda shi kuma ya amsa da cewa: “Na shirya wannan fim ne saboda ina ji a jikina cewa kayana ne na kashin kaina. Baya ga ingancinsa ta fuskar shiryawa a matsayin fim, labarinsa mai inganci ne. Yana dauke da tirka-tirka da fahimtarwa, nishadantarwa da kuma ilimantarwa. Bayan dukkan wadannan dalilai, ina tsammanin cewa akwai dalili na musamman, a matsayina na Musulmi, wanda yake rayuwa a kasashen Turawa, ina ganin cewa wajibina ne kuma hakkina ne in bayyana musu gaskiya game da Musulunci. Addini ne da yake da mabiya sama da miliyan 700, amma duk da haka a wannan bangare na duniya ba a san hakikanin gaskiyar bayani ba game da shi; wanda wannan abin ban mamaki ne a gare ni. Don haka ya zama wajibi in bayyana musu labarin addinin nan na gaskiya, domin su sani.”