Fintiri ga ’yan majalisar Adamawa:
Ba na tsoron a tsige ni Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ce shaida wa ’yan majalisar cewa idan sun isa su tsige shi domin ba ya tsoron a tsige shi. “Muna jiransu ko suna da kashi biyu a cikin ’yan majalisar jihar,” inji shi.Ahmadu Fintiri yana mayar da martani ne kan […]
Ba na tsoron a tsige ni
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ce shaida wa ’yan majalisar cewa idan sun isa su tsige shi domin ba ya tsoron a tsige shi. “Muna jiransu ko suna da kashi biyu a cikin ’yan majalisar jihar,” inji shi.
Ahmadu Fintiri yana mayar da martani ne kan yunkurin da ake zargin bangaren gwamnatin ya yi a ranar Litinin da ta gabata cewa za a tsige shi.
Ya ce niyyarsu ta tsige shi ya saba wa tsarin mulkin kasar nan, inda ya ce ’yan majalisar da ake son yin amfani da su, ba su isa su tsige shi daga mukaminsa na shugaban majalisar jihar ba.
“Duk wanda yake da gaba ko wata kullalliya tsakaninsa da shugaban majalisa ya fito ya fadi damuwarsa a majalisar. Ya kamata su tuna cewa mutane ne suka zabe ni, sannan ’yan majalisa suka zabe ne na zama shugaban majalisa ba wai kyautar kujerar wani ya ba ni ba,” inji shi.
Ya sake musanta kagen da aka yi masa cewa yana kokarin tsige Gwamnan Jihar Bala Ngilari. “Sun karbi kudi ne kawai a wajen ubangidansu kuma suna so su faranta wa mai gidansu rai,” inji shi.
Wasu ’yan da ke tare da dan majalisar Nasarawo/ Binyeri, Umar Abdulakarim sunace ’yan majalisa da dama sun dawo daga rakiyar Fintiri.
Abdulkarin ya bayyana cewa sun fara samun matsala ne da shi a lokacin da ya ce musu su hada kai su tsige Gwamna Bala Ngillari. Ya kara da cewa sun yi kuka da Fintiri in da ya rufe majalisar jihar domin bata wa ’yan majalisa rai kuma da tsoron kada a tsige shi.
“Wannan irin tsarin shugabanci na Fintiri ya sa muka dawo daga rakiyarsa don haka muna ganin bai cancanci ci gaba da zama a kan kujerarsa ba. Muna kira ga mutane da ’yan majalisa da jami’an tsaro da wadanda suka taimaka wajen rufe majalisar su bude ta domin ci gaba da aikinta a karkashin sabon shugabanta,” inji shi.
Da aka tambayi wani na hannun damar Gwamnan, Mista P.P. Elisha game da cece-kucen da ke faruwa a tsakanin bangaren Gwamnan da Fintiri, ya ce Gwamnan bai da hannu a zancen kuma a daina sa shi a irin wadannan maganganu marasa tasiri.“Ta yaya Gwamna wanda bai son tashin hankali zai yi kokarin tsige shugaban majalisa? A bar kowa da matsalarsa kada a sa Gwamna a ciki,” inji shi.