Fintiri ya rage ikon Lamiɗon Adamawa zuwa ƙananan hukumomi 3

Gwamantin jiahr ta rage ƙarfin ikon Lamiɗon Adamawa zuwa ƙananan hukumomi uku ta karɓe shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar daga hannunsa

Fintiri ya rage ikon Lamiɗon Adamawa zuwa ƙananan hukumomi 3

Lamido adamawa
(Tsohon hoto: www.flickr.com)

Gwamantin Jihar Adamawa ta tsige Lamiɗon Adamawa, Alhaji Mustapha Barkinɗo daga matsayinsa na Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar na Dindindin.

Kazalika ta ƙwace ikon naɗawa da tsige sarakuna daga hannunsa ta damƙa wa Gwamnan Jihar .

Haka kuma ta rage ƙasar Masarautar Lamiɗon Adamawa daga ƙananan hukumomi takwas zuwa uku: Girei da Jimeta da kuma Yola.

Shi ma Sarkin Mubi, Abubakar Isah-Ahmadu, za a rage masa faɗin masarutarsa mai ƙananan hukumomi biyar a ƙarƙashin wannan tsari.

Waɗannan na daga cikin abubuwan da sabuwar dokar masarautu da Majalisar Dokokin jihar ta amince da shi ranar Laraba.

A ranar Litinin Gwamna Ahmadu Fintiri ya gabatar da kuɗirin dokar neman ƙirƙiro sabbin masarautu da naɗa sarakuna a jihar.

Sabuwar dokar masarautun da ke jiran sa hannun Gwamna Fintiri ta mayar da shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar na karɓa-karɓa a tsakanin sarakunan yanka, na tsawon wa’adin shekara guda.

Sabuwar dokar masarautun ta samu karatun gaggawa daga Majalisar bayan da Gwmana Fintiri ya ƙirƙiro sabbon ya yankuna 83 masu dagattai.

Dokar, majalisar ta ce za ta tabbatar da adalci a tsakanin masarautun jihar da kuma kare tarihi da al’adu.

Masu adawa da ita kuma na ganin zai kassara tasirin masarautun jihar.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano