Fintiri zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a watan Agusta
Gwamnan ya amince da fara biyan ma’aikatan sabon mafi ƙarancin albashi a watan Agusta.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar, wanda zai fara daga watan Agusta.
Wannan na zuwa ne ta bakin Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) na jihar, Kwamared Emmanuel Fashe.
- Miliyan 29 ta yi wa Sanatoci kaɗan a wata — Sanata Abbo
- Cutar ƙyandar biri ba ta ɓulla a Gombe ba – Gwamna Inuwa
Fashe, ya sanar da haka ne bayan wata ganawar sirri da gwamnan a fadar gwamnatin jihar.
Fintiri tun da farko ya yi alƙawarin aiwatar da ƙudirin Gwamnatin Tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi a lokacin bikin Ranar Ma’aikata ta 2024.
Sai dai kuma Fashe, ya bayyana cewa ma’aikatan ƙananan hukumomi za su jira har zuwa watan Satumba kafin a daidaita albashinsu.
Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne, Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikata.