Fira Ministan Kanada ya saki matarsa bayan shekara 18 da aure
Fira Ministan da matarsa sun yanke hukuncin rabuwa bayan shekara 18 suna tare
Firaministan Kanada, Justin Trudeau da matarsa Sophie sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar rabuwa bayan kusan shekara 18 da aurensu.
Trudeau ya sanar da hakan ne a wani sako da ya wallafa ta shafin Instagram a yammacin ranar Laraba.
- ‘Kano na bukatar biliyan 6 don samar da kujerun zama a makarantu’
- Ministoci: Kano ta samu 2, Tinubu zai nada Matawalle, Bagudu, Lalong
“Jama’a, ni da Sophie muna so mu bayyana gaskiyar lamari, mun yanke shawarar rabuwa. Kamar yadda aka sani, mun zama dangi kuma za mu mutunta juna. Don jin dadin yaranmu, muna rokon a mutunta sirrinmu da sirrinsu. Na gode,” kamar yadda wallafa.
Kazalika, ofishinsa ya tabbatar da gaskiyar lamarin cikin wata sanarwa.
“Sun yi aiki don tabbatar da cewa an dauki dukkan matakan da suka shafi doka da da’a dangane da shawararsu ta rabuwa.
“Sun kasance dangi na kusa kuma Sophie da Firaminista sun mayar da hankali kan tarbiyyar ‘ya’yansu, cikin kauna da hadin gwiwa,” in ji sanarwar.
Trudeau mai shekara 51, da Sophie mai shekara 48, sun yi aure a watan Mayu 2005.
Allah Ya albarkace su karuwar yara uku.