Firaiministan Pakistan ya shiga dakin da aka binne Manzon Allah a Madina
An bai wa Imran Khan da matarsa damar shiga dakin da aka binne Fiyayyen Halitta.
Imran Khan bayan fitowarsa daga dakin da aka binne Manzon Allah (SAW)
Mahukunta Masallatan Alfarma na Saudiyya, sun bai wa Firaiministan Pakistan Imran Khan, damar shiga dakin da aka binne Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW) a masallacinsa da ke birnin Madina.
Shafin mahukuntan mai suna Haramai Sharifain ne ya bayyana hakan tare da hotunan Firaiministan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
- Mutum 8 sun rasu, 5 sun jikkata a hanyar Minna-Katsina
- Kumbon China da aka yi harsashen faduwarsa a Abuja ya rikito a Tekun Indiya
An bude wa Firaiministan tare da matarsa dakin da kabarin Manzon Tsiran yake yayin da suka ziyarci masallacin a ranar Lahadi.
Kazalika, a cikin dakin ne kuma akwai kaburburan Sahabbai biyu mafi falala na Manzon suke, wato Sayyadina Abu Bakr bn Saddiq da kuma Umar bn Khaddab, aminci ya kara tabbata a gare su.
Ingatattun tarihi sun bayyana cewa, bayan wafatin Manzon Allah, an binne shi ne a dakin matarsa, Nana Aisha RA, inda ya yi jinyarsa ta ajali kamar yadda al’ada ta tanadar na binne duk wani Annabi a inda ya rasu.
Kazalika, an binne halifofin biyu na Manzon Allah a kusa da kabarinsa bayan sun nemi alfarmar hakan daga wurin Nana Aisha.


