Firamaren Jigba a Abuja inda malami daya ke koyar da daukacin dalibai
Makarantar firamare ta kauyen Jigba da ke cikin tsakiyar wani daji a yankin Kuje da ke BirninTarayya, Abuja malami daya ne kacal wanda shi ma ba kwararre ba yake faman karantar da dalibai tun daga aji daya zuwa aji shida. Saboda rashin kyan hanyar zuwa kauyen da makarantar take, mota ba ta zuwa garin sai […]

Makarantar firamare ta kauyen Jigba da ke cikin tsakiyar wani daji a yankin Kuje da ke BirninTarayya, Abuja malami daya ne kacal wanda shi ma ba kwararre ba yake faman karantar da dalibai tun daga aji daya zuwa aji shida. Saboda rashin kyan hanyar zuwa kauyen da makarantar take, mota ba ta zuwa garin sai dai a babur ko keke ko dabbobi. Wannan malami daya da yake koyarwa a makarantar ya shafe tsawon shekaru shi kadai saboda karancin malamai.
kauyen Jigba yana da nisan kimanin kilomita 50 daga garin Kuje da kuma nisan kilomita kusan 70 daga garin Abaji. Garin yana da jama’a da dama da yara masu dimbin yawa. Al’ummar garin sun dogara da noma da kiwo a rayuwarsu.
Binciken Aminiya ya gano cewa Mista Emmanuel G. Gbegiya wanda gwamnati ta dauka a matsayin akawu wato Clarical Assistant, shi ne ya zama malamin makarantar inda yake koyarwa shi kadai a makarantar a shekaru masu yawa da suka gabata. Kuma ganin wannan hali ne, daga bisani kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) ta makarantar ta dauki wani matashi mai suna Shaban Zakka don taimaka masa, inda suke biyansa albashin Naira dubu 10 a wata.
Wakilin Aminiya ya tarar da Mista Emmanuel yana koyarwa shi kadai a makarantar tare da taimakon Shaban inda suke hada ajujuwa biyu zuwa uku a aji guda suna koyar musu da darasi.
Aminiya ta gano cewa kafin zuwan Shaban Ammanuel kadai yake koyar da dukan darussan a makarantar inda yake hada yaran makarantar a aji daya yana koyar musu darussa daban-daban. Yadda yake yi shi ne idan zai koyar da daliban aji daya sai daliban aji biyu su saurara sai ya kare, sai su kuma daliban aji daya su jira na aji biyu su dauki darasi haka zai rika yi har sai ya karantar da su baki daya.
Sai dai kuma a lokacin da Aminiya ta ziyarci makarantar don nemi karin bayani daga wurin Mista Emmanuel kan dalilin da ya sanya shi kadai ne malamin gwamnati da yake koyarwa a makarantar, sai ya ce ba zai ce komai ba saboda yana jin tsoron abin da ka iya biyo baya daga manyansa. Amma Mista Shaban Zakka da ke taimaka masa ya cewa shugaban makarantar ya tafi taro sannan mataimakinsa yana fama da rashin lafiya tsawon shekara biyu. Sai dai kuma har lokacin da Aminiya ta bar harabar makarantar zuwa lokacin da aka tashi daliban, shugaban makarantar bai dawo ba.
Kuma da Aminiya ta tsananta bincike sai ta gano cewa makarantar ba ta da shugaban makaranta, babu mataimaki kuma babu malami sai wannan malami daya na gwamnati. Shi ma rashin malami a makarantar ya sa ya bar aikinsa na akawu ya koma koyarwa a makarantar.
Malami mai taimakawa Mista Shaban ya bayyana wa Aminiya cewa “Rashin malami ne ya sa nake taimakawa. Na ga Mista Emmanuel shi kadai ne yake koyarwa a makarantar. Ni kuma dan asalin garin nan ne, shi ya sa na sadaukar da kaina nake koyar da yaran don kada a bar su haka nan. kungiyar Iyaye da Malamai ne suka dauke ni, kuma su ne suke biyana albashin Naira dubu 10 duk wata.”
To sai dai abin mamaki Mista Shaban Zakka da ke taimakawa, shi kadai ne ya mallaki takardar Malanta ta kasa (NCE) a kauyen na Jigba, amma ya koka cewa har yanzu bai samu aikin yi ba.
“Ni kadai na kammala karatun NCE a garin nan amma har yanzu ban samu aikin yi ba duk da kokarin da na yi na neman aikin. Na kai takarduna karamar Hukumar Kuje don su ba ni aikin koyarwa amma ban samu ba. Shi ya sa na yanke shawarar in rika koyarwa a makarantar kauyenmu don na taimaka wa ’ya’yana da kannena,” inji shi.
Ya bayyana cewa makarantar tana da dalibai kimanin 100, amma mutum daya ke koyar da su kafin ya shigo don taimakawa.
“Muna da dalibai sun kai 100 amma mu biyu ne muke koyar da su. Yadda muke yi shi ne mukan hada aji biyu zuwa uku a aji daya mu koya musu darasi. Nakan koyar da darasin tsafta da lissafi da motsa jiki da sauran darussa, shi kuma Emmanuel yakan koyar da Turanci da fannin addini da rubutu da sauransu. Amma wani lokaci idan ba ya nan ni nake koyar da dukkan darussan shi ma kuma idan ba na nan shi yake koyar da dukkan darussan,” inji shi.
Da yake jawabi kan batun, Sarkin kauyen Jigba, Mista Jatau Sarki, ya tabbatar da ikirarin da Shaban ya yi.
“Abin da Shaban ya gaya maka gaskiya ne, makarantarmu ba ta da malamai, a da akwai shugaban makaranta da mataimakinsa amma mataimakin ya daina zuwa saboda rashin lafiya da yake fama da shi. Mista Emmanuel da Shaban su ne suke taiamaka wa yaran. Saboda haka ina kira ga gwamnati ta taimaka mana da malamai,” inji sarkin.
Sai dai shugaban kungiyar ’yan asalin yankin Abuja, Fasto Jeji danladi, ya dage cewa malami daya ne yake koyarwa a makarantar Jigba shekara da shekaru kuma duk kokarin da suka yi na fadakar da gwamnati ta tura karin malamai ya ci tura.
“Malami daya ne yake koyarwa a makarantar firamaren Jigba. Ba shugaban makaranta babu mataimakinsa, babu wani malami a makarantar. Duk wanda ya gaya maka cewa akwai malamai ba gaskiya yake fadi ba. Ka je wurin ka gani da idonka. Mun sha gaya wa gwamnati ta tura karin malamai amma har yanzu ba su tura kowa ba,” inji shi.
daya daga cikin shugabannin iyayen yara na makarantar, Musa Biko, ya bayyana cewa sun dade suna sanar da gwamnati halin da suke ciki, amma ba ta yi musu komai ba.
“Gaskiya mun dade muna fuskantar karancin malamai kuma mun yi iya kokarinmu mun gaya wa gwamnati halin da muke ciki amma har yanzu ba su turo mana malami ba,” inji shi.
Shugaban kungiyar malamai reshen Birnin Tarayya, Abuja, Kwamared Hasan Jibir, ya ce, karancin malamai na daya daga cikin matsalolin da ke addabar makarantun yankin Abuja.
“Idan ka je makarantun da ke Abuja za ka tarar akwai karancin malamai akwai makarantun da za ka je a cikin gari ka tarar yawan daliban ya wuce kima kuma malami daya ne yake koyar da su kuma za ka tarar malami daya yana koyar da darussa masu yawa shi kadai. Ka ga wannan ya saba wa ka’idar koyarwa,” inji shi.
To, amma Babban Sakataren Hukumar Ilimin Bai-daya ta karamar Hukumar Kuje, Mista Sunday Kaka, ya musanta cewa malami daya neke koyarwa a makarantar ta Jigba.
“Ba malami daya ne yake koyarwa a makarantar Jigba ba. Akwai shugaban makaranta da mataimakinsa. Babu shakka muna da karancin malamai, amma kuma muna daukan matakan da suka kamata don maganin matsalar,” inji shi.
Shugaban karamar Hukumar Kuje, Honarabul Shaban Isiyaku Tete, ya bayyana cewa ya dauki malamai biyu a kowane kauye kuma nan ba da dadewa ba za su karbi takardunsu na aiki. “Daga cikin matakan da muka dauka don magance matsalar, mun dauki mutum biyu a kowane kauye don su koyar kuma nan ba da jimawa ba za mu ba su takardunsu na daukan aiki don su fara koyarwa a makarantun kauyukansu,” inji shi.