Firamaren Rafin Gora: Makarantar da ba ta taba yaye dalibi ba a shekara 40
Babban aikin da ke kan kowace gwamnati, shi ne kula da al’ummomin da take yi wa jagoranci, ta hanyar ba su tsaro da ilimi da kiwon lafiya da ruwan sha da hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa. To, amma ga al’ummomin garuruwan Rafin Gora da Unguwar Sule da Guraka da Yayaka da ke Gundumar Tama […]
Makarantar Firamare ta garin Rafin Gora da ba ta tava yaye dalibi ba a shekara 40
Babban aikin da ke kan kowace gwamnati, shi ne kula da al’ummomin da take yi wa jagoranci, ta hanyar ba su tsaro da ilimi da kiwon lafiya da ruwan sha da hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa.
To, amma ga al’ummomin garuruwan Rafin Gora da Unguwar Sule da Guraka da Yayaka da ke Gundumar Tama a Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, abin ba haka yake ba. Domin babu wani kayan more rayuwa, kama daga makarantu zuwa asibitoci da ruwan sha da hanyar mota da gwamnatin jihar ko karamar hukuma suka yi a garuruwan.
Ganin yadda gwamnati ta yi watsi da al’ummomin da yadda suka yi iyaka da Jihar Kano ya sa suka mayar da dukkan harkokinsu, zuwa Jihar Kano.
Da yake zanta wa da wakilinmu lokacin da ya ziyarci yankin, Sarkin Rafin Gora Malam Sa’adu Isah ya ce suna fama da matsalar hanyar mota a yankin, saboda shugabanni ba sa shigowa su ga halin da suke ciki.
Ya ce zamanin mulkin soja ana zuwa ana karce musu hanyarsu, amma yanzu da aka koma mulkin dimokuradiyya maimakon abin ya ci gaba sai ya yi baya.
Sarkin ya ce makarantar firamare ta garin wadda ta kai sama da shekara 40 da bude ta, babu yaron da ya gama makarantar saboda rashin malamai. Ya ce makarantar malami daya take da shi, wanda jama’ar garin ne ma suka dauke shi. Ya yi kira a taimaka a raya makarantar, ta hanyar gine-ginen ajujuwa kuma a samar mata da malamai.
Shi kuwa Sarkin Unguwar Sule Alhaji Alhassan Isah cewa ya yi babu shakka akwai matsalolin da suka damunsu a garin.
Ya ce suna fama da matsalar ruwan sha da hanyar mota kuma ba su da makarantar firamare a kauyen, kuma ba su da akwatin zabe.
Ya ce ba a taba kafa makaranta ba a kauyen, don haka dukkan yaransu suna shiga Jihar Kano ne domin yin karatu.
Ya ce ’yan siyasar Jihar Bauchi ba sa zuwa wajensu. “Don haka muka dauki ra’ayinmu muka kai Jihar Kano. Dukkan abubuwanmu baki daya mun koma Jihar Kano tun da ba a kula da mu a Jihar Bauchi. Domin babu abin da gwamnati ta taba yi mana a wannan kauye,” inji shi.
Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi da Karamar Hukumar Toro su gyara musu hanya a samar musu da makaranta da asibiti, kuma a dawo musu da akwatin zabensu da aka dauke.
Shugaban Kwamitin Raya Garin Unguwar Sule Alhaji Alhassan Idris ya shaida wa wakilinmu cewa babban dalilin da ya sa suka kafa kwamitin shi ne saboda gwamnati ba ta damu da su ba.
Ya ce sun kai kuka tun daga matakin sarakuna har zuwa shugabannin gwamnati, kan matsalolin da suke damunsu, amma duk da haka ba a yi musu komai ba.
“Don haka muka kafa wannan kwamiti, kuma a dalilin kwamitin mun samar da rijiyar burtsatse a garin. Kuma muna aikin gina makarantar firamare da kudinmu. Kuma mun tura yara da dama zuwa makaranta, wadansu har sun je sun yi karatun firamare da sakandare da NCE da Difloma a Jihar Kano.”
A zantawarsa da wakilinmu, Sarkin Guraka Alhaji Abdullahi Chindo ya ce suna da matsala game da asibiti da makaranta da hanyar mota da akwatin zabe a garin.
Ya ce ba a taba gina makaranta ba a garin, don haka kullum sai dai su kai ’ya’yansu makaranta Jihar Kano.
Ya ce maganar asibitin gwamnati da aka gina musu tun zamanin Shagari ya riga ya rushe, yanzu idan aka samu mara lafiya a garin sai dai su dauke shi su tafi Jihar Kano.
Ya ce a kan wannan asibiti ya je Toro ya kai sau biyar domin a ba su dama su samu ko wani gida ne a mayar asibiti amma abin ya gagara.
“Yanzu idan aka samu mara lafiya a garin na sai kai Jihar Kano. Amma duk lokacin da za a yi allurar foliyo sukan zo su yi mana,” inji shi.
Sarkin Yayaka, Malam Sa’idu Musa ya yi bayanin cewa suna fama da matsalar makaranta da asibiti da ya rushe a garinsa.
Ya ce idan rashin lafiya ya samu wani cikinsu sai dai su tafi Jihar Kano, inda ya ce idan kogi ya kawo a lokacin damina, sai dai su dauki mara lafiya a kai su haye da shi su tafi Jihar Kano.
To amma a zantawarsa da wakilinmu, Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Toro Alhaji Muhammed Yakubu Lame ya ce ba gaskiya ba ce, cewa ba a taba yaye dalibai a makarantar firamare ta garin Rafin Gora ba.
Ya ce babu yadda za a yi a ce an bude makaranta sama da shekara 40, amma ba a taba yaye dalibai ba. Sai dai a ce a ’yan shekarun nan ne ba a yaye dalibai ba, saboda rashin malamai.
Ya ce gaskiya laifin ma’aikatansu ne domin da suna da wannan labari, babu yadda za a yi tsohuwar makaranta irin wannan su kasa tura mata shugaban makaranta.
“Ba mu da labarin cewa wannan makaranta ba ta da malamai. Labarin da muke da shi akwai shugaban makarantar, amma ya yi ritaya. Tun daga shekarar 2015 malamai suna ta ritaya, ya kamata idan wadansu malamai suka yi ritaya a maye da wadansu. Amma saboda halin da gwamnati take ciki, sai ya zamanto ba a daukar malamai. Kuma yawaicin malaman da suke wadannan wurare sun yi ritaya, kuma ba a samu an sake daukar wadansu ba,” inji shi.
Kan asibitin Guraka da matsalolin kiwon lafiya da al’ummomin garuruwan suke fuskanta, Shugaban Sashin Kiwon Lafiya na Karamar Hukumar Toro Alhaji Ahmed Ibrahim Umar ya ce babu shakka lokacin da ya zo karamar hukumar shekara biyar da suka gabata, ya tarar da asibiti na Guraka a rushe.
Ya ce asibiti yana daya daga cikin asibitocinsu 6 da suka rushe, a yankin wanda gyara su ba zai yiwu ba, sai dai a sake gina sababbi.
Ya ce ko a sake gina asibitocin maganar kayan aiki da ma’aikata zai kawo tsaiko. Domin yanzu gina asibiti da samar da kayan aiki da ma’aikata, duk sun tashi daga karamar hukuma sun koma kan wata hukuma da aka kafa a jihar, wato Bauchi State Primary Health Care Debelopment Agency.
Ya ce yanzu asibiti 1,291 da ake da su a Jihar Bauchi suna karkashin wannan hukuma ce, ya ce ita ce take gina asibiti ta yi gyara ta bayar da kayan aiki kuma ta dauki ma’aikata.
Ya ce a baya matsalar Boko Haram ta sanya sun rufe asibiti 19 a yankin Lame domin ma’aikatansu da kayan aikinsu suna cikin hadari a lokacin.
Shugaban ya ce suna fama da matsalar karancin ma’aikata a sashin kiwon lafiya na karamar hukumar, domin idan aka kawo masu ma’aikata 500 a ba za su ishe su ba.
Wakilinmu ya ziyarci ofishin Hukumar Zabe (INEC) na Karamar Hukumar Toro, domin jin ta bakinsu kan kukan da mutanen garuruwan suke yi cewa an dauke akwatunan zabensu, amma bai samu babban jami’in ofishin ba. Amma wata majiya a ofishin ta tabbatar wa wakilinmu cewa ofishin ba su da wannan labari. Majiyar ta ce da ofishin suna da labarin da sun dauki matakin gyara.
Wakilinmu ya zanta da zababben dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Mazabar Lame, Bala Abdu Rishi kan wannan al’amari, inda ya ce babu shakka ya samu labarin halin da mutanen garuruwa suke ciki. Ya ce don haka ya je wuraren domin ya gane wa idonsa halin da mutanen suke ciki, domin ya taimaka.
Ya ce ya samu mutanen suna fama da matsalolin rashin makaranta da hanya da asibiti da ruwan sha, kusan babu wani abu na gwamnati a yankin.
Ya ba da tabbacin cewa idan ya je majalisa zai yi kokarin ganin ya kawo koke-koken wadannan mutane, domin a share musu hawaye kan matsalolin da suke damunsu.