Firaministan Bahrain ya rasu bayan shafe shekaru 49 a kan mulki

Firaministan Bahrain, Khalifa bin Salman Al Khalifa, ya rasu bayan shafe shekaru 49 a kan mulki.

Firaministan Bahrain ya rasu bayan shafe shekaru 49 a kan mulki

Tsohon Firaministan Bahrain, Marigayi Khalifa Bin Salman Al Khalifa

Firaministan Bahrain, Khalifa Bin Salman Al Khalifa, ya rasu bayan shafe shekaru 49 a kan mulki.

Khalifa, wanda ya fara mulkin kasar tun shekarar 1971 ya rasu yana da shekaru 84 a duniya, kamar yadda Babbar Kotun kasar ta sanar a ranar Laraba.

Kamfanin Dillacin Labarai na BNA ya rawaito cewa firaministan ya rasu ne a Asibitin Mayo dake jihar Minnesota ta Amurka.

Tuni dai Sarkin kasar ta Bahrain, Hamad bin Isa bin Salman ya mika sakon ta’aziyyarsa kan rasuwar tsohon firaministan

Ana sa ran gudanar da jana’izarsa da zarar gawarsa ta isa kasar, ko da dai ance ‘yan tsiraru daga cikin iyalansa ne kawai za a bari su halarta.

Sarkin kasar ya ba da umarnin a sauke tutocin kasar kasa-kasa yayin da ma’aikatu da hukumomin gwamnati za su kasance a rufe na tsawon kwanaki uku domin nuna alhini da rasuwar tasa.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa