Firaministan Iraki ya kori hafsoshin sojin kasar

A ranar Litinin da ta gabata ne Firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sallami manyan hafsoshin sojin kasar su 24 bayan bankado sojojin bogi guda 50,000 wadanda suke karbar albashi daga gwamnatin kasar. Firaministan ya ce ma’aikatan bogin sun haddasa wa gwamnatin kasar asarar dimbim miliyoyin daloli. Ya kara da cewa: “Na yi takaici matuka […]

Firaministan Iraki ya kori hafsoshin sojin kasar
Firaministan Iraki ya kori hafsoshin sojin kasar

A ranar Litinin da ta gabata ne Firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sallami manyan hafsoshin sojin kasar su 24 bayan bankado sojojin bogi guda 50,000 wadanda suke karbar albashi daga gwamnatin kasar.

Firaministan ya ce ma’aikatan bogin sun haddasa wa gwamnatin kasar asarar dimbim miliyoyin daloli. Ya kara da cewa: “Na yi takaici matuka saboda yadda gwamnatin ta ci gaba da biyan albashi a lokacin da ba mu da isassun kudi.”
“Muna da sojojin da suke fagen daga da kuma wadanda suka rasa rayukansu, a lokaci guda kuma mana da sojojin karya da suke karbar albashi,” inji shi.
kasar Iraki tana da sojojin da suka kai kimanin guda 800,000 kuma fiye da rabin miliyan da ciki dakarun musamman ne wadanda suke da horan soji, amma ba sa aikin sai ta-kwana. Wannan ya sa sojin kasar kimanin 300,000 ne suke cikin aikin sojin ka’in da na’in. Ana biyan kowane soja akalla Dala 600 a wata (kimanin Naira 100,000). Saboda haka kasar tana kashe kimanin Dala miliyan 380 a shekara.
Mai Magana da yawun Mista Abadi Rafid Jaboori ya ce an fara binciken ne da kigayar duka ma’aikata a lokacin biyan albashi. kasar Amurka wadda ta mamaye kasar na tsawon shekara takwas, ta kashe biliyoyin daloli wajen horar da samar da kayan aiki ga sojojin kasar. Tun lokacin da firaministan ya karbi mulki a watan Satumba, Mista Abadi ya sauke manyan kwamandojin sojin kasar. Kuma wannan matakin na ranar Litinin yana nuna yadda shugaban yake kokarin shawo kan cin hanci da karbar rashawa da suka yi kakagida a gwamnatin da ya gada ta Nouri al-Maliki.