Firaministan Iraki ya yi watsi da kafa gwamnatin hadaka a kasar
Firaministan kasar Iraki ya ce ba zai amince da matsin lambar kasashen duniya ba, akan bukatarsu ta kafa wata gwamnatin hadaka da ’yan Sunni da ke tawaye a arewacin kasar.Mista Maliki ya bayyana kiraye-kirayen da wani abu mai kama da juyin mulki a siyasance. Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a […]

Firaministan kasar Iraki ya ce ba zai amince da matsin lambar kasashen duniya ba, akan bukatarsu ta kafa wata gwamnatin hadaka da ’yan Sunni da ke tawaye a arewacin kasar.
Mista Maliki ya bayyana kiraye-kirayen da wani abu mai kama da juyin mulki a siyasance. Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a shekaranjiya Laraba, kwana guda bayan Sakataren Harkokin Wajen kasar Amurka, John Kerry ya bar kasar. Bayan wani shirin sulhu da ya jagoranta tsakanin shugabannin kurdawa da na ’yan Sunni da kuma na ’yan Shi’a.
Hakazalika, jawabin na zuwa ne bayan Amurka ta dauki alwashin cewa ba za ta kara aika wa da wani taimako zuwa Iraki ba, har sai bayan ’yan siyasar kasar sun hada gwamnatin hadin kan kasa.
A lokacin da yake jawabin na mako-mako wanda kuma aka yada a gidajen talabijin din kasar, Mista Maliki ya ce: “Kiraye-kirayen aiyana dokar ta baci a duk badin kasar wani abu ne da ya yi kama da juyin mulki ga kundin tsarin mulki da kuma tsarin siyasar Iraki. Wannan wani yunkuri ne da wadanda ba sa kaunar jaririyar dimukradiyyarmu suke fatan gani.” Inji shi.
A bangare guda kuma mayakan Sunni da kungiyar ISIS ke jagoranta, na ci gaba da nausawa birnin Bagadaza.