Firaministan Lesotho ya koma gida

A shekaranjiya Laraba ne Firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane ya koma gida bayan tserewar da ya yi zuwa kasar Afirka ta Kudu ranar Asabar da ta gabata.Mista Thomas ya gudu ne domin a cewarsa sojojin kasar sun kifar da gwamnatinsa, zargin da dakarun kasar suka musanta. Kodayake, kasashen duniya ba su  amsa kiran da ya […]

Firaministan Lesotho ya koma gida
Firaministan Lesotho ya koma gida

A shekaranjiya Laraba ne Firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane ya koma gida bayan tserewar da ya yi zuwa kasar Afirka ta Kudu ranar Asabar da ta gabata.
Mista Thomas ya gudu ne domin a cewarsa sojojin kasar sun kifar da gwamnatinsa, zargin da dakarun kasar suka musanta. Kodayake, kasashen duniya ba su  amsa kiran da ya yi ba tun farko, inda ya bukaci da su aike da dakaru don dawo da doka da oda a fadin kasar.
Ana dai tunanin cewa abin da ya haifar da rashin jituwa ba ya rasa nasaba da yadda firaministan yake samun goyon bayan ’yan sandan kasar. A bangare guda kuma  mataimakinsa Mothetjoa Metsing yana samun goyon bayan dakarun sojin kasar.
A cewar rundunar ’yan sandan kasar , rikici ya barke ne da safiyar Asabar bayan wata musayar wuta a wajen wasu ofisoshin ’yan sanda biyu da ke babban birnin kasar, Maseru. Artabun ya yi sanadiyyar mutuwar dan sanda daya, sai kuma wasu hudu da suka ji rauni.Wannan ya sa gidajen rediyon kasar dakatar da watsa shirye-shiryensu, da kuma katsewar layukan waya a kasar na sa’o’i da dama.
Mista Thabane shi ne shugaban kasar tun bayan kafa gwamnatin hadin kan kasa bayan zaben watan Mayun shekarar 2012, sai dai ya rushe majalisar dokokin kasar a watan Yulin da ya wuce, gudun ka da su tsige shi saboda yadda ake ci gaba da samun baraka a cikin gwamnatin hadakar.
kasar Lesotho kasa ce da ke a tsakiyar kasar Afirka ta Kudu kuma kewaye take da tsaunuka. kasar ta sha fuskantar juyin mulkin soji tun bayan samun ’yancin kanta a shekarar 1966.