Firaministan Libya zai yi murabus

Firaministan kasar Libya Ahmad Maiteg ya ce zai yi murabus saboda ya mutunta hukuncin Kotun kolin kasar wadda ta ce zabensa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.An dai zabe shi ne a watan jiya, a gaban majalisar dokokin kasar. Tun bayan zabensa, kasar ta ci gaba da samun firaminista biyu ne saboda tsohon firaministan […]

Firaministan Libya zai yi murabus
Firaministan Libya zai yi murabus

Firaministan kasar Libya Ahmad Maiteg ya ce zai yi murabus saboda ya mutunta hukuncin Kotun kolin kasar wadda ta ce zabensa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
An dai zabe shi ne a watan jiya, a gaban majalisar dokokin kasar. Tun bayan zabensa, kasar ta ci gaba da samun firaminista biyu ne saboda tsohon firaministan Abdullah al-Thinin ya ki ya sauka daga karagar mulki.
A wani jawabi da ya gabatar ga manema labarai ranar Litinin, jim kadan bayan hukuncin kotun kolin, Mista Maiteg ya ce shi ne zai zama mutum na farko da zai fara martaba hukuncin kotun. Inda ya ce: “Allah ya shaide ne, jama’ar kasar nan su shaida cewa na mutunta shari’a da kuma hukuncinta.”|
Abokin hamayyarsa Mista Thinin ya ce zai sauka a watan Afrilun da ya wuce saboda wani hari da aka kai wa iyalensa. Amma bai yi hakan ba saboda yadda a cewarsa aka gudanar da zaben Mista Maiteg, inda a lokacin wasu mahara suka ta da zaman majalisarsa.
Mista Maiteg, mai shekara 42, dan kasuwa ne da ya fito daga yankin Misrata. An shirya gudanar da wani sabon zaben a ranar 25 ga watan nan. Ko da yake bai kai ga bayyana ranar da zai sauka ba, amma an tsara cewa Mista al-Thinin ne zai ci gaba da zama firaministar rikon kwayar kasar kafin gudanar da zaben.