Firayi ministan Italiya zai turo jiragen yaki Jamhuriyar Nijar

Firayi ministan Qasar Italiya, Paolo Gentiloni ya ce zai isar da kudurinsa zuwa majalisar kasar domin ta amince ya debo wasu daga cikin mayakan da suke Qasar Irak ya dawo da su Jamhuriyar Nijar domin yaki da harkallar safarar mutane da ta’addanci. Gentiloni ya ce sojjoin Italiya da suke Qasar Iraki su 1,400 ne, don […]

Firayi ministan Italiya zai turo jiragen yaki Jamhuriyar Nijar

Firayi ministan Qasar Italiya, Paolo Gentiloni ya ce zai isar da kudurinsa zuwa majalisar kasar domin ta amince ya debo wasu daga cikin mayakan da suke Qasar Irak ya dawo da su Jamhuriyar Nijar domin yaki da harkallar safarar mutane da ta’addanci.

Gentiloni ya ce sojjoin Italiya da suke Qasar Iraki su 1,400 ne, don haka zai rago su tunda an samu nasarar fatattakar ’yan ta’addan kungiyar IS, domin a mayar da su yankin Afirka ta Kudu. Kamar yadda Reuter ta ruwaito.

“Ba mu ga ta zama ba. Dole mu ci gaba da mayar da hankalinmu da karfinmu wajen masu safarar mutane da ’yan ta’addan na yankin Afirka ta Kudu.

“Domin wannan matsalar, wasu daga cikin mayakanmu da suke Qasar Iraki za su koma Jamhuriyar Nijar a watanni masu zuwa. Wannan ne kudurin da gwamnati za ta mika wa majalisa,” in ji Gentiloni.

Sai dai bai yi cikakken bayani a kan mayakan guda nawa ne za su turo Nijar din ba, amma Jaridar Il Fatto Quotidiano ta ruwaito cewa mayakan za su kai “akalla 470”, kamar yadda yake cikin tsarin Shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Shugaban Faransa, Macron tuni ya ba da gudunmuwarsa wajen tallafa wa mayakan kasashen nan da ake kira G5, da suka hada da sojojin Mali, Mauritaniya, Nijar, Burkina Faso da Chadi wanda aka kaddamar a watan Oktoba domin dakile matsalar ta’addanci.

Domin tabbatar da shirin, Macron sai ya hada taro na musamman a ranar 13 ga watan Disambar, wanda ya samu halartar kasashen guda biyar, Jamus, Italiya da Saudiya.

Duk cewa ana tunanin majalisar Qasar Italiya za su kammala wa’adinsu a watan Maris, za su iya ci gaba da zama na musamman wanda hakan zai iya ba su dama su amince da kudurin Gentiloni na kaso sojojin.