Firayi Ministan Lebanon ya jingine murabus dinsa
Firayi Ministan Lebanon Sa’ad Hariri ya bayyana cewa ya jingine batun murabus dinsa, mako biyu bayan ya girgiza kasar da bayyana cewa zai sauka daga mukaminsa. Kafar labarai ta CNN ta ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa Hariri ya amince da bukatar Shugaban Lebanon Michel Aoun nay a jingine murabus din domin bayar da damar tuntuba […]

Firayi Ministan Lebanon Sa’ad Hariri ya bayyana cewa ya jingine batun murabus dinsa, mako biyu bayan ya girgiza kasar da bayyana cewa zai sauka daga mukaminsa.
Kafar labarai ta CNN ta ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa Hariri ya amince da bukatar Shugaban Lebanon Michel Aoun nay a jingine murabus din domin bayar da damar tuntuba a kan yunkurin.
A ranar 4 ga Nuwamba ne, Sa’ad Hariri ya bayyana niyyarsa ta yin murabus lokacin da ya je Saudiyya, inda ya ce, rayuwarsa tana cikin hadari. Lebanon ta ce ba za ta karbi murabus dinsa ba, sai ya dawo kasar. Kuma Shugaba Aoun ya yi zargin cewa an tsare Hariri ba bisa son ransa ba a Riyadh babban birnin Saudiyya, zargin da Saudiyya ta musanta.
A ranar Talata ce Hariri ya koma Lebanon, inda ya fara ziyartar kabarin mahaifinsa da aka kashe, tsohon Firayi Minista Rafik Hariri.
Magoya bayansa sun yi ta murnar dawowarsa, inda kuma a shekaranjiya ya halarci bikin faretin sojoji na ranar samun ’yancin kai tare da Shugaban kasar kafin ya gana da shi a fadar Shugaban kasa.
Rashin komawar Hariri kasar ta jefa kasar a cikin rudani da zaman dar-dar. Kuma kafin ya koma kasar sai da ya bi ta kasashen Faransa da Masar da Cyprus kafin ya wuce Beirut a ranar Talata.