Firayiminista ya bai wa wadanda suka ci jarabawar sakandire mamaki

Firayiministan Hadaddiyar Daular Larabawa, Shaikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, ya bai wa wadanda suka cinye jarrabawarsa ta kamala sakandare  mamaki, inda ya rika kiransu ta waya, yana bayyana musu sakamakon jarrabawarsu, sannan ya taya su murna.“Taya murna ga daliban da suka samu nasara ya sanya sun kasance cikin farin ciki da karin kwarin gwiwa/ […]

Firayiminista ya bai wa wadanda suka ci jarabawar sakandire mamaki
Firayiminista ya bai wa wadanda suka ci jarabawar sakandire mamaki

Firayiministan Hadaddiyar Daular Larabawa, Shaikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, ya bai wa wadanda suka cinye jarrabawarsa ta kamala sakandare  mamaki, inda ya rika kiransu ta waya, yana bayyana musu sakamakon jarrabawarsu, sannan ya taya su murna.
“Taya murna ga daliban da suka samu nasara ya sanya sun kasance cikin farin ciki da karin kwarin gwiwa/ Wannan zai sanya kasarmu ta kara ci gaba a fagen ilimi. Don haka muna alfahari da wadanda suka samu maki mai tsoka, muna cike da farin cikin taya iyalansu murna. Muna yi musu fatan samun nasara a sauran ayyukan nazarin kimiyya da gwaje-gwajen da za su gudanar a rayuwarsu.
daliban da ya kira sun hada da Sarah Abdul Rahim Al Emadi, ta makarantar sakandaren Maria Al kibtiyya School, wadda ta fi kowa cin maki a fannin zane-zane da maki 99.75 cikin 100; sai Hazim Mahmoud daga makarantar sakandare ta Madhab  da kle Masarautar  Fujairah wanda ya ci maki 99.93  cikin 100 a fannin kimiyya.  Sai Abdullah Mahmoud Abdullah Ahmed na makarantar  Mohammed bin Hamad Al Sharki School da ke Fujairah  wadannan su suka fi kowa yin fice da lashe maki a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Shaikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, a amtsayinsa na mataimakin Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, shi mutunm ne wanda ya damu da duk wata harka da ta shafi ilimi.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda