Firayiministan Ukrain ya roki afuwar ’yan adawa
Firayiministan kasar Ukrain, Mykola Azrob ya roki afuwar masu zanga-zangar kan yadda hukumomin kasar suka yi amfani da ’yan sanda wajen shawo kan tarzomar. Ya fito ya roki ’yan adawa da su daina ruruta wutar rikici, domin a cewarsa, wannan shi ne rikicin siyasa mafi muni da kasar ke fama da shi a tsawon shekara […]

Firayiministan kasar Ukrain, Mykola Azrob ya roki afuwar masu zanga-zangar kan yadda hukumomin kasar suka yi amfani da ’yan sanda wajen shawo kan tarzomar. Ya fito ya roki ’yan adawa da su daina ruruta wutar rikici, domin a cewarsa, wannan shi ne rikicin siyasa mafi muni da kasar ke fama da shi a tsawon shekara 10 da suka gabata. Kuma ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya yi taron majalisar mulki, tun bayan da zanga-zanga ta addabi gwamnatinsa.
Mutum dubu 350 suka yi wa gwamnati zanga-zangar adawa, a tituna da dandalin ’yanci da ke birnin Kieb, tun farkon makon da ya gabata, inda suke adawa da ficewar gwmnati daga ’yarjejeniyar shiga Tarayyar Turai. Shugaban kasa, biktor Yanukobych, ya fice daga ’yarjejenioyar da aka shirya kullawa tsakanin Tarayyar Turai da kasar Ukrain, inda ya fifita alakarsa da kasar Rasha.
Matsalar da ta haifar da rikicin siyasar Ukrain, ita ce shiga Tarayyar Turai, inda mafi yawan al’umma ke ganin kasar za ta samu shigowar masu saka hannun jari, yayin da ita kuwa gwamnati ke ganin gara ta ci gaba kulla alaka da tsohuwar uwar gijiyarta, kasar Rasha.
“Ina kira da a shawo kan rura wutar rikicin siyasa,” a cewar Azrob, a daidai lokacin da ya fara taron majalisar ministocinsa, kuma masu zanga-zanga suka yi yunkurin tare hanyoyin shiga hedkwatar ofisoshin gwamnati.