Firayiministan Yemen ya roki ’yan Facebook su zabo masa ministoci

Sabon Firayiministan Yemen Khaled Bahah, ya roki masu amfani da shafukan Facebook da su gabatar masa da sunayen ministocin da suka kamata ya nada. Wannan kuwa ya biyo bayan amincewar da ya samu daga jam’iyyun siyasar kasar da suka bukaci shi da Shugaban kasar Rabbo Mansour Hadi su kafa sabuwar gwamnati. Saboda Firayiministan Khaled Mahfoud […]

Firayiministan Yemen ya roki ’yan Facebook su zabo masa ministoci
Firayiministan Yemen ya roki ’yan Facebook su zabo masa ministoci

Sabon Firayiministan Yemen Khaled Bahah, ya roki masu amfani da shafukan Facebook da su gabatar masa da sunayen ministocin da suka kamata ya nada. Wannan kuwa ya biyo bayan amincewar da ya samu daga jam’iyyun siyasar kasar da suka bukaci shi da Shugaban kasar Rabbo Mansour Hadi su kafa sabuwar gwamnati.

Saboda Firayiministan Khaled Mahfoud Bahah, wanda tsohon jakadan kasar ne a Majalisr dinkin Duniya, an nada shi kan wannan mukami ne bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘’yan tawayen al-Houthi.
Bahah ya sanar da masu mu’amala da shafukan sadarwa da su taimaka masa wajen zabo kwararrun ministoci masu mutunci.
“Shigo cikin ’yan kasa wajen gabatar da sunayen kwararrun ma’aikata ga gwamnati don kaima a dama da kai,” a cewar Baha, a wani sako da ya baza a shafinsa na Facebook, wanda ya samu masu sha’awar sakonsa har mutum dubu 18 da 882.
Wannan sako da ya aike ya jawo ra’ayin dubban mutane da suka rika yin sharhi, har ma suka gabatar masa da sunayen mutanen da ra’ayinsu ya damfaru a kai, don a kafa sabuwar gwamanti tare da su.
Sannan an bijiro masa da sunan Janar Mahmoud al-Sobihi,kwamandan rundunar sojan rukuni na hudu da ke Aden, a matsayin ministan tsaro. Wasu masu mu’amala da shafukan sun shawarci Bahah da ya ci gaba da aiki da ministan harkokin cikin gidan kasar, Janar Abdo al-Tarab.
Masu mu’amala da kafar sadarwar da dama sun nuna bukatar ganin an zabi.
Shi kuwa Mounir al-Mawari, wani dan jarida, dan asalin kasar Yemen da ke zaune a kasar Amurka, ya shawarci sabon Firayiministan da kada ya nada wani mutum kan mukami, matukar ya taba kasancewa a cikin jami’an tsohuwar gwmanatin da ta gabata.
“Ina shawartarka kan yin watsi da jami’an tsohuwar gwamnatin da ta gabata, kafin ma ka aikata komai, tunda gwamnati ce da ta gaza,” inji shi.
Duk da haka,wasu daga cikin masu amfani da shafin Facebook din ba su gabatar masa da sunaye ba, amma sun yaba wa kokarinsa na gabatar da wannan muhimmin al’amari a kafafen sadarwar na Intanet.