Firayiministar Austireliya ta fadi zabe, tana saka wa jaririn sarautar Birtaniya kayan wasa
Firayiminista Gillard ta Austireliya ta fadi zaben Shugabancin jam’iyya a lokacin da take dinka wa jaririn gidan sarautar Ingila kayan wasa masu siffar akuyar kangaru. Julia Gillard ta bayyana yadda take saka jan kangaroo ga jaririn farko da Yarima William da Gimbiya Kate za su Haifa.“Dangane da sakar da take yi wa jaririn Kate Middleton […]
Firayiminista Gillard ta Austireliya ta fadi zaben Shugabancin jam’iyya a lokacin da take dinka wa jaririn gidan sarautar Ingila kayan wasa masu siffar akuyar kangaru. Julia Gillard ta bayyana yadda take saka jan kangaroo ga jaririn farko da Yarima William da Gimbiya Kate za su Haifa.
“Dangane da sakar da take yi wa jaririn Kate Middleton kuwa – ina yin saka ga jarirai, a wani lokaci, domin kananan ayyuka ne, kuma ba ni da cikakken lokaci a tsawon rayuwata,” inji Misis Gillard, kamar yadda ta bayyana wa wata mujalla da ta yi hira da ita.
Mist Kebin Rudd ya kayar da Firayiminista Julia Gillard a zaben shugabancin Jam’iyyar Labour ta kasar Austiraliya, don haka wannan mace mai kamar maza za ta bayar da wuri nan da watan Satumba mai zuwa, da zaran an gudanar da zaben kasa.
Julia Gillard ita ce macen farko da ta taba zama Firayiminista a Austiraliya, amma Mista Rudd, wanda shi ma tsohon Firayiminista ne ya sake kwato kujerarsa, inda zai jarraba sa’arsa ta neman shugabancin kasar a karo na uku, nan da watanni uku masu zuwa.
kuri’un da aka kada wajen zaben shugabancin jam’iyyar, Mista Rudd ya samu kashi 57 cikin 100, yayin da Gillard ya karke da kashi 43 cikin 100, kamar yadda jami’in zaben ya bayar da sanarwa. Nasarar Rudd ta sanya a shiga dar-dar a jam’iyyar Labour, inda ake gudun kada Jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Conserbatibe, a karkashin jagiorancin Tony Abbott ta yi musu fintikau, a zaben 14 ga Satumba.
Misis Gillard za ta shawarci Gwamna-Janar kuentin Bryce cewa za ta yi murabus a matsayin Firayiminista, tun a ranar Alhamis din da ta gabata, kafin a rantsar da Mista Rudd.