Firayiministar Thailand na kokarin shawo kan ’yan adawa 1

Firayiministar kasar Thailand na kokarin shawo kan ’yan adawa da ke yi mata zanga-zanga, inda ta ziyarci ofishinta a karo na farko, bayan da zanga-zangar ’yan adawa ta sanya ta gudu. Zanga-zangar ta yi kamari cikin kwanaki biyar da suka wuce, sai dai kokarin da take yi na nuna wa mutane cewa al’amura sun saisaita, […]

Firayiministar Thailand na kokarin shawo kan ’yan adawa 1

 Masu zanga-zanga a kasar ThailandFirayiministar kasar Thailand na kokarin shawo kan ’yan adawa da ke yi mata zanga-zanga, inda ta ziyarci ofishinta a karo na farko, bayan da zanga-zangar ’yan adawa ta sanya ta gudu. Zanga-zangar ta yi kamari cikin kwanaki biyar da suka wuce, sai dai kokarin da take yi na nuna wa mutane cewa al’amura sun saisaita, sai kwatsam wata zanga-zangar ta sake barkewa, inda aka yi wa hedkwatar ’yan sanda kawanya.
Masu zanga-zangar, sun amince a dakata na kwana daya, don karramar sarkin kasar, Bhumibol Adulyade dan shekara 86, a lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, a Alhamis din da ta gabata, amma sun jajirce kan cewar za su ci gaba da yi wa gwamnati matasin lamba, da zarar an kamala bikin ranar haihuwar sarki.
Duk da cewa masu zanga-zangar sun yanke cewa za su ci gaba da zanga-zangar lumana, amma sai da suka kawar da shingayen wayoyi da jami’an tsaro suka kakkafa, har ma sai da suka yi yunkurin haurawa tsakiyar hedkwatar ’yan sanda da ke Bangkok, wanda ke kusa da katafaren kantin sayar da kakayyaki na kasar mafi Irma.
Ganin haka, ’yan sanda sun bude kofofin shigarsu don wasu daruruwan mutane masu zanga-zanga su samu shigowa ciki, bayan da suka nuna sun samu nasara, sai masu zanga-zangar suka fice daga wurin salun alun.
Hukumomin kasar sun yi amfani da lalama irin yadda ’yan sanda suka kwatanta don shawo kan masu zanga-zanga, wadanda suka mamaye ofisoshin gwamnati
Ana ganin wannan yunkurin da gwamnatin ke yi, mafita take nemar wa kanta, ta yadda za a shawo kan wannan rikici da ya dabaibaye kasar, al’amnarin da ya haifar da asarar rayuka hudu tare da jikkata mutum 256.
Ranar haihuwar sarkin kasar, ranar hutu ce ta kasa, don haka kowa na jira da sauraren jawabin sarki da zai gabatar a tashar taabijin, ta yadda zaz a san amtsayar fada a kan rikicin siyasar kasar.
Bhumibol sarki ne da ked a muhalli a kundin tsarin mulkin kasar, sai dai bas hi da wnai mukami na siyasa, amma duk da haka ya sha yin tasiri wajen kwantar da rikice-rikicen da suka rika tasowa a baya. Kuma al’ummar kasar na ganin cewa tayar da tarzom ko zanga-zanga a ranar tunawa da hibhuwar sarki tamkar nuna rashin girmamamawa ne.
Shugaban ’yan adawar Suthep thaugsuban ya jajirce wajen cin alwashin kawar da gwamnatin Yingluck, ta yarda zai kawar da tasirin dan uwanta, tsohon Firayiminista, Thaksin Shinawatra daga harkokin siyasar kasar. Domin yana kallont aa matsayin karyar farautar Thaksin, wanda aka kawar da gwamnatinsa a juyin mulkin soja na shekarar 2006.