Firimiyar Ingila: Arsenal ta lallasa Brighton
Arsenal na jan ragamar gasar da maki 71 bayan buga wasan mako na 32.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta doke Brighton Hove & Albion da ci uku da babu a wasan mako na 32 na Gasar Firimiyar Ingila.
Ɗan wasan gaban Arsenal, Bukayo Saka ne, ya fara jefa mata ƙwallo a minti na 33 a bugun fanareti.
- EFCC ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan Emefiele
- Sojoji za su iya kawo ƙarshen matsalar tsaro — Kwankwaso
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Arsenal ta sake jefa ƙwallo a minti na 62, ta hannun Kai Havertz, sai kuma Lisandro Trossard da ya ƙara ƙwallo ta uku a minti na 86.
Arsenal dai na ci gaba da jan ragamar gasar da maki 71, kafin Liverpool ta kara da Manchester United a ranar Lahadi.
Manchester City na mataki na uku a teburin gasar da maki 70, bayan ta doke Crystal Palace da ci 4 da biyu a ranar Asabar.
Tsakanin Arsenal, Liverpool da Manchester City za a samu wadda za ta zama zakara a ƙarshen gasar Firimiyar Ingila ta bana.
Ana ci gaba da kai ruwa rana a tsakanin ƙungiyoyin uku, inda kowace ke yin gudun yada-ƙanin wani.