Fitaccen dan fim Joseph Ruskin ya mutu

Joseph Ruskin, fitaccen dan fim a Amurka ya mutu a makon da ya gabata. Ya mutu ne yana dan shekara 89 a duniya, a ranar 28 ga Disambar bara; a asibitin UCLA Medical Center, Santa Monica, Amurka.A yayin da yake raye, Joseph ya kasance dan fim mai kokari a sana’arsa ta fim. Ya fito cikin […]

Fitaccen dan fim Joseph Ruskin ya mutu

Marigayi Joseph RuskinJoseph Ruskin, fitaccen dan fim a Amurka ya mutu a makon da ya gabata. Ya mutu ne yana dan shekara 89 a duniya, a ranar 28 ga Disambar bara; a asibitin UCLA Medical Center, Santa Monica, Amurka.
A yayin da yake raye, Joseph ya kasance dan fim mai kokari a sana’arsa ta fim. Ya fito cikin fina-finai 25, sannan fito cikin wasannin kwaikwayo na talabijin 124. Wasu daga cikin fitattun fina-finansa sun hada da ‘The Magnificient Seben’ da ‘Prizzi’s Honor.’ Wasannin kwaikwayonsa na talabijin kuwa sun hada da ‘The Twilight Zone’ da ‘Star Trek’ da ‘Alias.’
Saboda dadewarsa a harkar fim, Ruskin ya dade cikin hukumar zartarwa ta kungiyar ’Yan Wasa daga 1976 zuwa 1999. Sannan kuma shi ne mutum na farko da ya rike mukamin mataimakin shugaban kungiyar na tsawon shekara takwas. Cikin kyaututtukan karramawa da ya samu kuwa, sun hada har da Kyautar Karramawa ta Morgan, a 2011 da Kyautar Karramawa ta Lucy Jordan a 2013 da kuma Kyautar Karramawa ta Parick kuinn, a 2013.
Marigayin, ya nazarci al’amuran wasannin kwaikwayo a Jami’ar Carnegie-Mellon, a lokacin tana matsayin Carnegie Tech. Ya fara harkar wasan kwaikwayo a gidan wasa na Pittsburg Playhouse, kafin daga bisani ya koma gidan wasa na Rochester Arena Stage. A karshen rayuwarsa, ya yi wasa ne a gidan wasa na Antaeus Theater, a shekarar da ta gabata.
dan wasan dai ya mutu ne ya bar matarsa, Barbara Greene Ruskin da ’yarsa, Alicia Ruskin da surukinsa, Larry Buckland da kuma agololinsa, Rachel Greene, Martha Greene da Liza Pag.

Marigayi Farooq Sheikh… Haka shi ma jarumin Indiya Farook Sheikh

A ranar Asabar da ta gabata ce, daya daga cikin jaruman fina-finan Indiya, Farook Sheikh ya rasu.
Marigayin ya shahara a sana’arsa ta fim, inda ya yi fice a fina-finan ‘Chashme Buddoor’ da ‘Garam Hawa’ da kuma na baya-bayan nan, ‘Yeh Jawaani Hai Deewani.’
Farook ya rasu ne da safiyar Asabar a birnin Dubai, inda ya je da nufin hutu. Ya mutu ne a sakamakon ciwon zuciya da ya sarke shi.
Marigayin, an haife shi ne a ranar 25 ga Maris, 1948. Ya fara fim dinsa na farko ne a 1973, inda ya fito a wani fim mai dauke da jigon siyasa, mai suna ‘Garam Hawa’ (Zazzafar Iska). Fim din yana bayyana matsalolin da wasu iyali, Musulmi suke fuskanta, a sakamakon raba Indiya da aka yi da Pakistan.
’Yan fim da dama da suka san shi kuma suka yi sana’a tare, sun bayyana shi a matsayin mutum na kwarai. Shahararriyar ’yar fim, Shabana Azmi, wacce ta sha fitowa cikin fina-finai tare da marigayin, a lokacin da take jimamin mutuwarsa, ta ce: “Zuciyata ta karye. Zumuntarmu da shi ta faro ne tun daga kwaleji kuma tare muka fara sana’ar fim. Babu shakka zumuntarmu ta faro da dadewa, don haka abu ne mai wahala in iya yin wata magana game da Farook a wannan yanayin.”
Gawar marigayi Farooq, a lokacin da ake nufin kai ta kushewaShi kuwa dan fim Shekhar Kapur, a tasa ta’aziyyar wadda ya yi a turakarsa ta Twitter, cewa ya yi: “A haduwar mu da shi ta karshe, mun tattauna ne game da al’amuran siyasa. Da na sani da mun tattauna game da sana’armu ta wasan kwaikwayo, domin kuwa abin da muka fi kauna ke nan a rayuwarmu. Da mun yi haka da shi, lallai da na koyi ilimin sana’ar mai yawa daga gare shi.”