Fitaccen dan kasuwa a Kano Sani Yakasai ya rasu
An yi jana’izar sa a Kofar Kudu ta Fadar Sarkin Kano.
Babban dan kasuwa kuma fitaccen dan kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin dai shi ne shugaban kamfanin gine-gine na SDY, wanda yana daya daga cikin jiga-jigan kamfanonin kwangila a jihar da kewaye.
- Madrid ta soma nazarin dauko Haaland daga City
- Shugaba Xi ya sha rantsuwar ci gaba da mulkin China a wa’adi na uku
A cewar wata majiya, Alhaji Yakasai ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Majiyar ta kara da cewa, Yakasai ya rasu yana da shekaru 68 a duniya kuma ya bar matansa da ’ya’yansa da jikoki.
An yi jana’izar sa a Kofar Kudu ta Fadar Sarkin Kano da misalin karfe 8 na safiyar wannan Juma’ar, sannan an binne gawarsa a makabartar Tarauni.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje; Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero da Sanata Ibrahim Shekarau, na daga cikin dimbin musulmin da suka halarci jana’izar dan kasuwan wadda ya rasu a jiya Alhamis.