Fitaccen dan sara-sukar da ya addabi Zariya ya mutu
daya daga cikin ’yan sara-sukan da suka addabi jama’a garin Zariya da kewaye da ke Jihar Kaduna mai suna Salisu Yakubu da aka fi kira da Mai Sammatsi ya mutu, lamarin da ya sa mutanen birnin da kewaye murna. Mai Sanmatsi wanda yake zaune a Kwanar Shahada a Unguwar Jushi da ke kan hanyar Jos […]

daya daga cikin ’yan sara-sukan da suka addabi jama’a garin Zariya da kewaye da ke Jihar Kaduna mai suna Salisu Yakubu da aka fi kira da Mai Sammatsi ya mutu, lamarin da ya sa mutanen birnin da kewaye murna.
Mai Sanmatsi wanda yake zaune a Kwanar Shahada a Unguwar Jushi da ke kan hanyar Jos zuwa Zariya, kamar yadda shugaban ’yan sintiri na Masarautar Zazzau Alhaji Kabiru Amadu ya shaida wa Aminiya, tun kusan shekara uku da suka wuce shi da jama’arsa suka addabi mutanen Zariya da kewaye musamman mutanen Jushe.
Ya ce sakamakon ayyukan su Mai Sammatsi mutane da dama sun fara sayar da gidajensu suna barin unguwar, “kuma shi wannan yaro Mai Sammatsi yana da daba wadda ta addabi kowa wajen sace-sace da yi wa yara mata fyade, har daukar ’yan mata suke yi da sunan ’yan daukar amarya,” inji shi.
Ya ce haka suke ta yi har zuwa ranar da suka dauki wata yarinya da sunan daukar amarya kusan wata bakwai ana nemanta ba a ganta ba, “Sai a ranar Asabar da ta gabata muka ga yarinyar inda muka kai ta ofishin ’yan sanda na Zariya domin bincike, kuma ana cikin bincike ne sai ga wasu ’yan mata biyu sun zo wanjen ta sai aka kama su aka hau bincike,” inji shugaban ’yan sintiri wanda ya kara da cewa “Muna cikin haka sai Mai Sammatsi ya bugo wa daya daga cikinsu waya ya ce ta same shi a wani wuri, sai muka dora ta a kan babur na sa yara biyu suka bi su, muka bi su a mota, ashe dama inda suke sun tara makamai kamar su gariyo da adda da sauransu, koda suka ga yarana sai kawai suka hau su da sara suka ji wa yarana biyu, Amadu da Abdulkarim, ciwo yanzu haka suna asibiti, nan muka far musu muka kama shi bayan ba-ta-kashi sannan muka dauko shi zuwa ofishin ’yan sanda, bayan ya gama jawabi sai aka dauke shi zuwa asibiti daga baya muka ji ya cika.”
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta baklin iyalan marigayin amma abin ya ci tura.
Sai dai wani jami`in ’yan sanda da bai so a ambaci sunansa ya tabatar da aukuwar lamarin inda ya koka kan yadda iyayen yara ke daure musu gindi suna ta’asa ga jama’a.