Fitaccen dan siyasa Tony Anenih ya kwanta dama

A ranar Lahadin da ta gabata ce Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje, Tony Anenih ya rasu. Marigayi Anenih ya rasu yana da kimanin shekara 85 a duniya a wani asibiti da ke Abuja bayan ya sha fama doguwar jinya. Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da al’ummar jihar Edo da kuma […]

Fitaccen dan siyasa Tony Anenih ya kwanta dama

A ranar Lahadin da ta gabata ce Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje, Tony Anenih ya rasu. Marigayi Anenih ya rasu yana da kimanin shekara 85 a duniya a wani asibiti da ke Abuja bayan ya sha fama doguwar jinya.

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da al’ummar jihar Edo da kuma jam’iyyar PDP, yana mai cewa Najeriya ta yi rashin babban gwarzo kuma hazikin dan kasa. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, ta ce an yi rashin babban jigo wajen hada kan ‘yan kasa a Najeriya.

Shi ma dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce mutuwar Tony Anenih wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyarsu ta PDP babban rashi ne, kuma ba za a taba mantawa da irin gudunmuwar da ya bayar ga jam’iyyar ba.

Kazalika jam’iyyar PDP ma ta bayyana alhininta bisa ga rashin da suka yi, inda a cikin shafinta na Twitter ta ce, ta kadu matuka bayan samun labarin rasuwar Tony Anenih.

An haifi Mista Anenih ne a jihar Edo, kuma yana daga cikin masu fada aji a cikin siyasar Najeriya, ya rike mukamai da dama a jam’iyyun siyasar kasar nan, ciki har da shugaban jam’iyyar NPN a jiharsa a shekarar 1981 zuwa 1983, inda har ake ganin ya taka muhimmiyar rawa a zaben 1983 mai cike da ce-ce-ku-ce a tsohuwar jiharsa ta Bendel a wancan lokaci, inda ya taimaka wa Samuel Ogbemudia ya samu nasara.

Kazalika Tony Anenih ya rike mukamin shugaban jam’iyyar SDP na kasa a shekarar 1993. Haka kuma ya kasance daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP, inda a nan ne har Shugaba Olusegun Obasanjo ya bashi mukamin ministan ayyuka da gidaje. Baya ga haka ya kasance daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na jam’iyyar ta PDP ya mutu ya bar mace daya da kuma da daya.