Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu

Dokta Dutsen Tanshi ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman magani a ƙasashen Masar da Saudiyya.

Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu

Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan gaskiya.

Almajiransa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a gidansa da ke Bauchi inda za a yi jana’izarsa a safiyar wannan Juma’ar.

Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman magani a ƙasashen Masar da Saudiyya.

Fitowarsa ta ƙarshe ita ce ranar Idin ƙaramar Sallah da ta gabata, inda ya yi huɗuba kan muhimmanci haɗin kai a tsakanin musulmi.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa