ICPC ta tsare D’banj kan kudin N-Power
ICPC ta tsare D’banj, ne bisa zargin karkatar da kudaden shirin tallafin matasa na N-Power
Hukumar Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC) ta tsare fitaccen mawakin Najeriya, Oladapo Daniel Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’banj.
Rahotanni sun nuna a ranar Talata ICPC ta tsare D’banj, domin bincikar sa, bisa zargin karkatar da kudaden shirin tallafin matasa na N-Power.
- Kotu ta daure Mataimakiyar Shugaban Kasar Argentina
- Yadda hatsarin mota ya jefa Abuja cikin duhu
- DAGA LARABA: Jabun Kayayyaki: Ina Hukumar SON Ta Shiga Ne?
Rahotanni sun nuna an ga fitaccen lauyan kare hakkin dan Adam, Pelumi Olajengbesi a ofishin ICPC da taek tsare da mawakin.
Wasu majiyoyi sun ce Pelumi Olajengbesi lauya ne ga D’banj, wanda ake wa lakabi da The Koko Master.