Fitar da jadawalin zabubbukan 2019 da Hukumar zabe ta yi

A makalata ta makon da ya gabata nayi bayanin cewa shekarar nan da muka shiga ta 2018, shekara ce da za ta zama ta karshe ga gwamnatocin da wa’adinsu zai kare ranar 29-05-2019, don haka ita ce shekararsu ta karshe da za su iya gudanar da ayyukan raya kasar da suka yi ma al’ummominsu alkawarin […]

Fitar da jadawalin zabubbukan 2019 da Hukumar zabe ta yi

A makalata ta makon da ya gabata nayi bayanin cewa shekarar nan da muka shiga ta 2018, shekara ce da za ta zama ta karshe ga gwamnatocin da wa’adinsu zai kare ranar 29-05-2019, don haka ita ce shekararsu ta karshe da za su iya gudanar da ayyukan raya kasar da suka yi ma al’ummominsu alkawarin aiwatarwa a lokacin yakin neman zaben 2019, kasancewar shekara mai zuwa ita ce shekarar babban zaben kasar. Sai ga shi kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC, a ranar Talatar da ta gabata bayan wani taro da Hukumar ta yi a Abuja, ta kuma kira taron manema labarai, inda ta yi bayani filla-filla a kan abin da jadawalin zabubbukan shekarar 2019, ya kunsa.

A karkashin jaddawalin, Hukumar ta INEC, ta tsaida ranar Asabar 16-02-2019, ta zama ranar da za ta gudanar da zabubbukan shugaban kasa da na ‘yan Majalisun dokoki na kasa, wato Sanatoci da na Majalisar wakilai. Yayin da na gwamnoni da ‘yan Majalisun dokoki na jihohi zai biyo baya da kwanaki 14, wato zai kasance a ranar 2-03-2019, tare da na Majalisun kananan hukumomi 6, da su ke babban birnin tarayya Abuja. Hukumar ta INEC, ta kebe tsakanin 18 ga watan Agusta zuwa ranar 3 ga watan Oktoban bana da za su zama kwanakin da ta deba wa dukkan jam’iyyun siyasa da suke da kwadayin shiga zabubbukan da su gudanar da zabubbukan fitar da gwanayensu da kuma karkare dukkan rikice-rikicen da ka iya biyo bayan fitar da ‘yan takarar na su kafin cikar wancan wa’adi. Yayin da makamancin irin wannan zabe ga ‘yan takarar da suke sha’awar shiga takarar zabubbukan Majalisun kananan Hukumomi na babban birnin tarayyar Abuja Hukumar ta INEC ta ce a karkaresu tsakanin 4 ga watan Satumba zuwa ranar 27 ga watan Satumban banan.

Furofesa Mahmood Yakubu ya fadi cewa jam’iyyun siyasar za su karbi fom na tsayar da ‘yan takara daga 11 zuwa 24 ga watan Augustan bana, yayin da za su karbar wa ‘yan takararsu masu neman mukamin Majalisun kananan Hukumomi na babban birnin tarayyar Abuja tsakanin ranar 3 zuwa 10 ga watan Nuwamban banan. 

Mai karatu ka ga ke nan daga yadda shugaban hukumar ta INEC, Furofesa Mahmood Yakubu ya bayyana jaddawalin zabubbukan badin, a wannan shekara kenan harkokin siyasa a kasar nan za su kankama ka’in da na’in ke nan, ba wai sai shekarar 2019, ba. Don haka kamar yadda na ambata a sama, duk gwamnatin da ba ta da aikin da za ta nuna wa mutanenta a zaman cikasa alkawurran da ta yi a zabubbukan 2019, za ta fuskanci babban kalubale a cikin yakin neman zaben wannan karon. Zabubbukan 2019, zabubbuka ne da ake sa ran akalla koda bisa ga yawan jam’iyyun siyasa 68, da ake da su a cikin kasa a daidai wannan lokaci, ba a kuma san karin jam’iyyun siyasa da hukumar zaben ta INEC, za ta kara yi wa rijista nan gaba, kasancewar Furofesa Mahmood Yakubu ya ce a yanzu haka akwai jam’iyyu 90, da suka mika bukatun a yi musu rijista. Ka ga ke nan mai karatu koda yawan wadanan 68, da ake da su yanzu kadai aka ce za su shiga zabubbukan kasar akwai gagarumin aiki ga su kansu shugabannin jam’iyyun da Hukumar zaben dama sauran masu ruwa da tsaki wajen samun nasarar wannan gagarumin aiki mai matukar muhimmancin gaske a cikin mulkin dimokuradiyyar kasar nan da ake yanzu kusan shekaru 20, ba kakkautawa. 

Ya kuma kamata mai karatu ya sa ni cewa a jihohi 29, da babban birnin tarayyar Abuja, in ban da zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Osun da Ekiti da Ondo da Edo da Anambra, hukumar ta INEC, za ta gudanar da zabubbukan na shekarar 2019, inda za a zabi shugaban kasa 1, da Sanatoci 109, da ‘yan Majalisar wakilai ta tarayya 360, da na ‘yan Majalisun jihohi su 991, adadin wadanda za a zaba a badin ke nan zai kai 1558.      

Ana kuma san rai kafin nan da wadannan zabubbuka Majalisun dokokin kasar nan za su yi gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, kamar yadda aka yi masa kwaskwarima a baya, musamman bisa ga neman ra’ayoyin ‘yan kasa da dukkan ‘yan Majalisun dokoki na tarayya suka gudanar a karshen shekarar 2013, a dukkan mazabunsu 360. Daga cikin batutuwan da aka yi muhawara akai har da batun neman a ba da dama ga dan takara mai zaman kansa ya tsaya takarar neman kowane irin mukami da yake bukata, koda kuwa na shugaban kasa ne. 

Zabubbukan na badi ana kyautata zaton su fi na shekarar 2015, sahihanci, duk kuwa da na shekarar 2015 din, shi ya kawar da babbar jam’iyyar PDP a wancan lokacin daga kan karagar mulki da take kai har tsawon shekaru 16, ba kakkautawa. A wajen bayyana wancan jaddawalin zabe a rawaito shugaban Hukumar ta INEC, ya roki ‘yan siyasar kasar nan da su tabbatar da cewa za su gudanar da dukkan harkokinsu na wadannan zabubbuka cikin kwanciyar hankali da lumana, yana mai nuni da cewa zabubbukan 2015, sun zama wani zakaran gwajin dafi a wannan dimokuradiyya ta kasar nan, abin da ya ce Hukumarsa a shirye take wajen ganin ta dora a kan nasarorin wancan zabe. 

Daga dukkan alamu masu ruwa da tsaki a cikin harkokin siyasar kasar nan sun yi maraba da yadda Hukumar ta INEC, ta fitar da wancan jadawalin, alal misali Majalisar ba da shawara akan harkokin siyasar kasar nan, wato IPAC, tuni ta yi maraba akan yadda Hukumar ta INEC, ta fitar da tsarin zabubbukan badin da wuri da kuma irin yadda za su kasance. Ita ma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta bakin Kakakinta Mista Kola Olugbondiyan manema labarai sun rawaito shi yana cewa “A zaman mu na jam’iyya, muna maraba da jaddawalin zabubbukan da Hukumar ta INEC, ta shirya kuma ta gabatar ma da kasa. Wannan wani abin maraba ne.” in ji Mista Kola.

Sanin kowa ne nasarar zabubbukan siyasa a duk duniya ba ta dogara a kan Hukumar da ke shirya su yi ta kadai. Dukkan dan kasa nagari yana da hakkin ya tabbatar da cewa an yi su lami lafiya, bisa ga irin mihimmancin da suke da shi a ci gaban kowace kasa da mutanenta. Don haka tunda Hukumar zabe ta bayar da tabbacin za ta gudanar da wadannan zabubbuka cikin kamanta gaskiya da adalci, to, kuwa kamar yadda ta nema dukkan masu ruwa da tsaki kan al’amarin, to su ma su ba da tasu gudunmuwar yadda ta kamata. A nan akwai bukatar shugabannin jam’iyya su daina yin kama-karya da nuna dagawa, musamman wajen tsayar da ‘yan takara. Da wannan ke nan ake bukatar a bari jama’a su darje akan wanda suke so ya tsaya musu takara ba a rinka yi musu kama-karya ba. Samuwar hakan za su yi matukar rage yawan matsaloli da rigingimu da kan sa har a je kotu bayan zabubbuka. 

Alkalan kasar nan suna da gagarumar rawar da za su taka a wadannan zabubbukan 2019, musamman wajen ganin ba su rinka bayar da hukunce-hukunce marassa kan gado a cikin kararrakin zabe, musamman na dakatar da gudanar da su gab da lokacin da za a kada su. Da wannan na ke fatan dukkan ‘yan kasa za su ba da gudunmuwarsu gwargwadon zarafi wajen samun nasarar zabubbukan badin. Allah ka ba mu ikon zaben shugabanni nagari tun daga sama har kasa.