Fitattun waƙoƙin siyasa da suka yi tasiri a wannan jamhuriyya

Yau Nijeriya riko sai mai gaskiya, Baba Buhari kai muke so Nijeriya.

Fitattun waƙoƙin siyasa da suka yi tasiri a wannan jamhuriyya

A ranar 29 ga Mayu ne Nijeriya ta cika shekara 25 da komawa mulkin dimokuraɗiyya kuma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara guda a karagar mulki.

A makon jiya Aminiya ta ruwaito yadda mawaƙa suka taimaka wajen tallata ’yan takarar siyasa tun a siyasar Jamhuriyar ta Farko.

A wannan mako za mu rairayo wasu fitattun waƙoƙin siyasa ne da suka yi tashe sosai, ake ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen tallata jam’iyyu da ’yan takararsu a wannan Jamhuriyya ta Huɗu.

1999

A 1999 Jam’iyyar PDP ta fafata a za&e da jam’iyyun APP da AD, bayan wasu kusoshin ’yan siyasa sun haɗu sun kafa ta.

Fitaccen mawakin nan Haruna Aliyu Ningi daga Jihar Bauchi ya wake jam’iyyar kuma da wakar mai cewa, “PDP jam’iyyata, a bar so a zukata, mutanen Nijeriya ku taso mu rike ta,” jam’iyyar ta yi yawon kamfe har ta samu nasara.

Kuma ya yi wakar “PDP muke so ku zo ga jam’iyya. Ku sa ta a zuciya al’ummar Niijeriya.”

A tattaunawa da Aminiya, mawaki Haruna Ningi ya bayyana dalilin yin wakokin, inda ya ce, “Kafin Janar Abacha ya rasu akwai manyan mutane da na yi wa waka, kamar su marigayi Alhaji Abubakar Rimi da Alhaji Sule Lamiɗo da Alhaji Isa Yahaya Zarewa da Alhaji Kabir Ɗambatta duk na fara hulɗa da su a lokacin.

To bayan Janar Abacha ya rasu, sai waɗannan mutane iyayen gidana da aka kakkama, sai aka ce za a fito da jam’iyya.

To kafin a fito da jam’iyyar sai na zauna na yi nazari cewa tunda waɗannan iyayen gida nawa ’yan siyasa ne duk jam’iyyar da za su fito ni ma a ciki zan fito.

Sai na fara nazari na tsara wa Jam’iyyar PDP wakoki nau’o’i uku.

Lokacin da aka zo kaddamar da Jam’iyyar PDP a Ningi, su Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi da tsohon Gwamna Ahmadu Mu’azu da sauran shugabannin PDP suka hallara a nan ne na fara rera wakar siyasa a gaban jama’a.

Da suka ji ta yi, sai suka ce suna bukatar in buga ta, lokacin marigayi Shettiman Katagum (Alhaji Bashir Mustapha), da Baraden Bauchi (Alhaji Umaru Ɗahiru) lokacin yana Sakataren Jam’iyyar shi ya ba ni sunayen shugabannin jam’iyyar ya ce in kai masa kaset ɗin.

To daga nan aka fara baza wakar. To da su aka yi ta amfani a kasar Hausa wajen yaɗa Jam’iyyar PDP.

Sai dai ya ce a lokacin bai ci gajiyar wakar ba sai daga baya, a shekarar 2021 Alhaji Atiku Abubakar ya ba shi kyautar mota.

2003

A shekarar 2003 ce tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shigo siyasa a Jam’iyyar ANPP bayan sauya mata suna daga APP.

Wakarsa da ta yi tashe a shekarar ita ce wakar da har yanzu ake yi mata lakabi da Bakandamiyar Buhari wato wakar Malam Ibrahim Yala ta, “Yau Nijeriya riko sai mai gaskiya, Baba Buhari kai muke so Nijeriya.”

Haka a shekarar 2007 ya sake sabunta wakar, wadda da ita aka cigaba da kamfe da ita.

A shekarar 2011 ce Buhari ya koma CPC, inda a nan Malam Yala ya rera masa wakar, “CPC Jam’iyyar Buhari, mai alkalamin da bai rubuta karya.”

A shekarar 2015 kuma aka samu mawakan Hausa  suka shiga siyasa dumu-dumu, kasancewar a lokacin Masana’antar Kannywood ta fara tabarbarewar saboda rashin kuɗi.

A shekarar ce aka fara samun mawaka suna haɗuwa domin tallata ɗan siyasa.

Wakar “Lema ta yage” ce ta fito da wata sabuwar salon tallata ’yan siyasa, inda Forodusa Abdul Amart ya tattara mawaka da ’yan fim masu yawa suka wake Buhari da Jam’iyyar APC.

Kafin wannan haɗakar, Haruna Ningi ya yi watsi da Jam’iyyar PDP, inda ya yi mata wakar, “Shegiyar uwa mai kashe ’ya’yanta PDP.”

Haruna ya taɓa bayyana wa Aminiya cewa a can baya, “Mutanen da suka kafa Jam’iyyar PDP suka yi wahalar kafa ta su ake kora daga jam’iyyar.

“To ni a matsayina na dillalin da ya yi tallar ta, bai kamata in zuba ido abubuwa suna tafiya haka ba, dole in yi wani abu da zai kare jam’iyyar.

“Ba wanda ya sa ni in yi wakar, a cikin jiga-jigan PDP akwai ma wanda ya yi kokarin kada in saki wakar ta Shegiyar Uwa,” in ji shi.

Sai mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fara kunno kai. Kafin shekarar ya yi wakoki a siyasar Kano, irin su “Ba da ni ta ɓare ba” a lokacin zaɓen 2007 da sauransu.

Amma wakarsa ta “Zuwan Mai malfa Kano” ta shahara sosai.

Sannan ya biyo bayanta da “Masu gudu su gudu,” bayan Buhari ya ci zaɓe. Tun wancan lokaci ne mawakin yake kan kandami, wanda har ake kallon shi ne mawakin siyasa da ya fi samun nasara.

A Zaɓen 2019 mawaka sun karu a harkar siyasa, inda ake sake yin haɗakar wakar Buhari.

Amma wakar “Abba Gida-Gida Abba” ta Tijjani Gandu tana cikin wakokin da suka fi ɗaukar hankali.

A siyasar 2023, Kannywood da rabe, inda mawaka da dama suka koma wajen Atiku wasu kuma suka tsaya a APC sannan wasu na Kwankwasiyya. A APC ma aka samu tsagin Rarara da tsagin Abdul Amart.

Wakar Rarara ta “Jagaba shi ne gaba” ta yi tashe sosai.

Sannan ya yi wasu wakokin irin su, “Hello Hello” da “ Sai Kashim sai Tinubu.”

A ɓangaren PDP kuma Nura M. Inuwa ya yi wakar, “Arewa bana ta ɗinke mu bar wa su Baba Atiku rikon kasa.”

Mabiya addinin gargajiya sun nemi a riƙa rantsuwa da gumakansu Alhaji Abbas ya ce, akasarin ƙananan hukumomin ƙasar nan suna ƙarƙashin shugabancin kwamitocin riƙo, wanda hakan na taimakawa wajen ƙarin samar da rashin tsaro.

Daliin da gwamnoni ba sa son ba ƙananan hukumomi ’yanci-Shugabannin majalisun jihohi

Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohi na Ƙasa, Mista Adebo Ogundoyin wanda shi ne shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo ya ce, dalilin da ya sa gwamnoni ba sa son ƙananan hukumomi su samu ’yancin kansu, shi ne tsoron Gwamnatin Tarayya za ta yi amfani da su a matsayin makami a kansu.

Kuma ya ce idan aka ba ƙananan hukumomin ’yancin kuɗaɗensu za su fuskanci ‘ƙarancin kuɗi musamman a ƙananan hukumomin karkara.

“Wannan zai haɗu da almubazzaranci da dukiya ko almundahana. Kuma ƙaramar hukuma za ta riƙa samun umarni daga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tarayya,” in ji shi.