Fitattun ’yan kwallo 6 da suka Musulunta

1.  Emmanuel Adebayor:  Adebayor haifaffen Togo ne wanda yake buga wa kulob din Tottenham na Ingila kwallo.  Ya yi kwallo a kulob da dama a Nahiyar Turai ciki har da kulob din Real Madrid.  Yanzu haka yana kokarin canza sheka ne zuwa kulob din Aston billa na Ingila.  Emmanuel Adebayor ya karbi shahada ne a […]

Fitattun ’yan kwallo 6 da suka Musulunta
Fitattun ’yan kwallo 6 da suka Musulunta

1.  Emmanuel Adebayor:  Adebayor haifaffen Togo ne wanda yake buga wa kulob din Tottenham na Ingila kwallo.  Ya yi kwallo a kulob da dama a Nahiyar Turai ciki har da kulob din Real Madrid.  Yanzu haka yana kokarin canza sheka ne zuwa kulob din Aston billa na Ingila.  Emmanuel Adebayor ya karbi shahada ne a watan jiya kamar yadda jaridar Aminiya ta kalato muku labarin.  Kuma dan kwallon ya Musulunta ne a kasar haihursa watau Togo inda aka gan shi yana karbar shahada daga wajen wani malamin addinin Islama da ke kasar.  Jim kadan da faruwar hakan ce sai labarin Musuluntar dan kwallon ta watsu a kafofin watsa labarai ciki har da na shafin zumunta na facebook da na twitter da sauransu.  Duk da cewa har yanzu dan  kwallon bai fito karara ya bayyana wa duniya labarin Musuluntarsa ba, rahotanni sun tabbatar dan kwallon ya karbi addinin Islama a wata cibiyar yada addinin Musulunci da ke Togo. A da dan kwallon yana bin akidar Katolika ce ta addinin Kirista kafin ya Musulunta a watan jiya. Tuni wadansu kafofin watsa labarai suka ruwaito dalilai 13 da suka sanya ya Musulunta, don haka za a iya cewa yanzu ya fito karara ya bayyana wa duniya cewa shi Musulmi ne.

2. Franck Ribery:  Ribery dai shahararren dan kwallon Faransa ne da yanzu haka yake buga kwallonsa a kulob din Bayerrn Munich da ke Jamus.  Rahotanni sun tabbatar dan kwallon ya karbi addinin Musulunci ne a shekarar 2002 inda ake kyautata zaton matarsa Wahiba Belhami Balarabiya ita ta ja ra’ayinsa har ya Musulunta.  Tuni dan kwallon ya kara sunan Bilal a jerin sunayensa don ya tabbatar wa duniya labarin musuluntar tasa.  Amma har yanzu an fi kiransa da Franck Ribery ne saboda sabo.  Tuni dan kwallon ya ce ya samu natsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsa tun bayan da ya Musulunta kimanin shekaru 13 da suka gabata.  Don haka babu tantama, Ribery Musulmi sabanin yadda wadansu ke tababa.

3.  Eric Abidal Eric:  Tsohon dan kwallon Faransa da kuma kulob din FC Barcelona na Sifen.  Ya daina buga kwallo ne saboda matsalar ciwon zuciya.  A shekarar 2011 ce likitoci suka gano dan kwallon yana fama da matalsar ciwon zuciya sannan a shekarar da ta zagayo ne kuma aka yi masa aiki bayan an yi masa dashen sabuwar zuciya al’amarin da ya tilasta shi yin ritaya daga buga kwallon kafa.  A shekarar 2007 ce Abidal ya Musulunta jim kadan bayan ya yi aure inda ya canza sunansa zuwa Bilal Eric Abidal.  Rahotanni sun tabbatar dan kwallon ya karbi addinin Musulunci ne saboda matarsa Hayet Kebir ’yar asalin Aljeriya wacce ake gani ita ta shawo kansa har ya karbi addinin Islama.

4. Emeka Ezeugo:  Emeka Ezeugo, tsohon dan kwallon baya ne a kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles. Yana daga cikin ’yan kwallon da suka yi wa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya da ya gudana a Amurka a shekarar 1994.  A watan Fabrairun 2012 ne dan kwallon ya koma Musulmi bayan ya karbi shahada.  Kamar yadda Ezeogu ya nuna a wata hira da aka yi da shi, ya karbi addinin Musulunci ne bayan ya gamsu da rayuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Ya ce ya gamsu da tarihin Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) don haka ya karbi addinin Islama.

5.  Nicolas Anelka:  Shi ma Anelka, tsohon dan kwallon Faransa ne.  Yanzu haka yana buga wa kulob din Indiya mai suna Mubai City FC ne a matsayin dan kwallo da kuma manaja.  Rahotanni sun tabbatar dan kwallon ya Musulunta ne  tun yana da shekara 16 a duniya. Sai dai bai bayyana wa duniya ainihin addinin da yake bi ba sai daga baya.  A shekarar 2004 ce ya firo kara ya shaida wa duniya cewa shi Musulmi ne daga nan ne kuma ya canza sunansa zuwa Abdul-Salam Bilal amma har yanzu an fi kiransa da Nicolas Anelka saboda sabo..

6.  Danny Blum:  Shi kuma Danny dan kwallon Jamus ne.  A watan Janairun wannan shekara da muka ciki ne dan kwallon ya bayyana wa duniya labarin Musuluntarsa.  A wata tattaunawa da aka yi da shi a Jamus Danny ya nuna yana yin salloli biyar a rana, sannan ba ya ci ko shan abincin da Musulunci ya haramta.  Ya bayyana Musulunci a matsayin addinin kwanciyar hankali da samar da zaman lafiya.
Sai dai da yawa daga cikin mutane sun dauka shahararren dan kwallon Holland da yanzu haka ya koma kulob din Fenerbahce na Turkiyya daga kulob din Manchester United na Ingila Robin ban Persie Musulmi ne.  Gaskiyar al’amari ba Musulmi ba ne duk da yake yana auren ’yar kasar Maroko mai suna Bochra.  Abin da ya sa aka tabbatar dan kwallon ba Musulmi ba ne shi ne a wata hira da aka taba yi da shi ya ce “Ni ba Musulmi ba ne, ba kuma Kirista ba ne sannan ba Pegan ba ne”, ma’ana ba shi da addinin da yake bi.  Wadannan kalamai sun tabbatar dan kwallon ba Musulmi ba ne kamar yadda wasu ke yayatawa.
Shi ma shahararren tsohon dan kwallon kulob din Arsenal na Ingila wanda ya yi kwallo a kulob da dama irin su Monaco da Jubentus na Faransa da FC Barcelona na Sifen da kuma New York Red Bulls da ke Amurka Theirry Henry an tabbatar ba Musulmi ba ne.  Sai dai wani rahoto da aka taba kalato wa na kan kwallon ya taba bayyana cewa ya fi kusa da addinin Islama fiye da kowane irin addini a duniya. Wannan kalami ne ta sa wadansu suka dauka cewa dan kwallon Musulmi ne.  Sai dai akwai alamun dan kwallon zai iya karbar addinin Islama nan gaba ganin irin take-takensa na rungumar al’amarin Musulunci fiye da kowane irin addini.  Hasalima, dan kwallon yana da abokai Musulmi masu yawa kuma ya nuna a duk lokacin da zai karbi wani addini, to babu addinin da zai karba da ya wuce na Islama.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja