Fitattun ’yan kwallon da suka koma Saudiyya da taka leda

Koulibaly ya bayyana cewa saboda kasancewar yana bukatar kudi sosai ya yanke shawarar komawa Saudiyya.

Fitattun ’yan kwallon da suka koma Saudiyya da taka leda

Tun a tsakiyar kakar bara da fitaccen dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo ya koma kasar Saudiyya da taka leda bayan ya raba gari da Kungiyar Manchester United, sai gasar kasar ta kara armashi a idon masoya kwallo.

Duk da cewa fitattun tashoshin talabijin da suke nuna wasannin kwallon kafa na duniya ba sa nuna gasar ta Saudiyya, masoya dan wasan da wadanda ba sa son shi, suna bibiyar kafar YouTube domin ganin yadda take kayawa da shi da Kungiyar Al Nassr da ya koma da wasa.

A daidai lokacin da za a fara kakar bana, kungiyoyin kasar ce suka rikita kasuwar hada-hadar ’yan wasa, inda suka yi ta taya manyan fitattun ’yan wasan duniya da kudi mai yawa.

Dan wasan kasar Senegal Koulibaly ya bayyana cewa saboda kasancewar yana bukatar kudi sosai da zai ci gaba da daukar dawaniniyar iyalansa da ’yan uwansa da kuma wasu ayyuka da yake so ya yi a kauyen da ya fito, da kuma kasancewarsa Musulmi ne suka sa ya yanke shawarar komawa Saudiyya da buga kwallo.

Wani abu da ya tayar da kura shi ne yadda dan wasa Cristiano Ronaldo ya yi sujada bayan zura kwallo a wani wasa a kasar, inda aka rika yada hoton sujadar ana bayanai a kai Aminiya ta bibbiyi yadda kungiyoyin kasar suke rububin sayen fitattun ’yan kwallo zuwa yanzu.

Karim Benzema:

Daga Real Madrid zuwa Al Ittihad Karim Benzema, wanda shi ne Gwarzon Dan Kwallon Duniya na yanzu ya bar Kungiyar Real Madrid ta Spain duk da cewa sun bukaci ya kara sanya hannu a kwantaragi domin ci gaba da zama kungiyar inda ya koma Al Ittihad ta Saudiyya.

Barin Real Madrid ya yi matukar zuwa wa magoya bayan kungiyar da ba-zata, kasancewar shi ne Kyaftin, sannan ba a samu shakku ba a kan kasancewarsa wanda yake jan ragamar kungiyar, ballanta a fara tunanin ajiye shi a benci.

Ya koma Kungiyar Al Ittihad ce wadda ta lashe Gasar Firimiyar Saudiyya ta bara, inda ya sanya hannu a kwantaragin shekara uku a kan Fam miliyan 107 duk shekara, kudin da suka ninka kudin da yake samu a Real Madrid.

Da yake bayani a lokacin gabatar da shi ga magoya bayan kungiyar, Karim farawa ya yi da sallama, sannan ya ce a matsayinsa na Musulmi ya ji dadin komawa Saudiyya da taka leda, sannan ya ce kasancewar Cristiano Ronaldo, wanda ya bayyana a matsayin abokinsa a gasar kasar ya sa ya samu saukin yanke shawarar.

N’Gole Kante:

Daga Chelsea zuwa Al Ittihad Shi ma Kante, wanda dan kasar Faransa ne ya koma Kungiyar Al Ittihad domin ci gaba da taka leda tare da dan kasarsa Karim Benzema.

Kante yana cikin ’yan wasan kasar Faransa da suka lashe Gasar Kofin Duniya a shekarar 2018, sannan zai rika karvar albashin Fam miliyan 86 duk shekara a kwantaraginsa ta shekara hudu.

Ruben Neves:

Daga Wolves zuwa Al Hilal Shi ma dan wasan Kungiyar Wolverhampton Wanderers ko kuma Wolves a takaice, wanda dan asalin kasar Portugal ne, ya bi sahun Kyaftin din kasarsa Cristiano zuwa Saudiyya, inda ya koma Kungiyar Al Hilal, wadda ita ce kamar Real Madrid a yankin Asiya wajen lashe kofuna da kafa tarihi. Neves ya koma kungiyar ne a kan Fam miliyan 60

Kalidou Koulibaly:

Daga Chelsea zuwa Al Hilal Koulibaly ya bar Kungiyar Chelsea kaka daya bayan zuwansa daga Napoli a kan Fam miliyan 42, inda suka sayar da shi yanzu ga Kungiyar Al Hilal a kan Fam miliyan 20.

Hakim Ziyech:

Daga Chelsea zuwa Al Nassr Hakim, dan wasan kasar Moroko ya amince ya koma Kungiyar Al Nassr domin ci gaba da wasa tare da Cristiano Ronaldo.

Tuni wasu suke ganin hadin zai yi kyau, kasancewar an san Ziyech da iya jefa kwallo, shi kuma Ronaldo an san shi da iya jefa kwallon a raga.

Sai dai kuma dan wasan bai samu damar kulla kwantaragi da kungiyar ba yayin da aka gano ba shi da koshin lafiya sakamakon wani rauni a gwiwarsa.

Edourd Mendy:

Daga Chelsea zuwa Al Ahli Shi ma Golan Chelsea ya koma Kungiyar Al Ahli bayan ya sha fama da zaman benci a Kungiyar Chelsea a kakar bara.

Dan wasan wanda ya lashe Gasar Kofin Afirka da kasar Senegal ya koma kungiyar da take Jiddah, inda za su fafata a wasa mai zafi (derby) da abokinsa kuma Kyaftin din kasar Koulibaly.

Wasu wadanda ake zawarcinsu a kasar su ne Neymar Jnr, wanda Al Hilal ke zawarcinsa daga Kungiyar PSG ta Faransa, sai Roberto Firminho wanda ya bar Kugiyar Liverpool bayan ya zura kwallo 110 a wasa 361, duk da cewa Barcelona ma tana zawarcinsa.

Akwai kuma Saul da Kungiyar Al Nassr ke zawarcinsa daga Kungiyar Atletico Madrid da Bernado Silva da Al Hilal ke zawarcinsa daga Kungiyar Manchester City da Marcelo Brozovic da Al Nassr ke zawarcinsa daga Inter Milan, wanda saura kiris ne ma ya koma kungiyar ta Saudiyya.