Fitattun ’yan wasa 29 da suka koma Saudiyya
Yawancin ’yan kwallon nan talakawa ne, suka samu dama suka daga darajar gidansu da kwallon.
A daidai lokacin da kakar bana ta kwallo take kankama, kuma aka rufe hada-hadar ’yan wasan, Aminiya ta lura a bana an yi kasuwancin ’yan wasan a kasar Saudiyya.
Wannan ya sa wasu suke tunanin an cire shauki da kaunar kwallon kafa a zukatan ’yan wasa, inda suka muhimmantar da samun kudi fiye da suna.
- Mun kashe ’yan ta’adda 52 a Borno da Yobe — DHQ
- Diphtheria: Cutar mashaƙo ta yi ajalin mutum 10 a Jigawa
Masu sharhi suna ganin ba son kwallon da burin inganta harkar kwallon a Saudiyya ba ne suka sa ’yan wasan suka yi tururuwar zuwa kasar ba, illa makudan kudin da ake ba su fiye da abin da suke samu a Turai.
Wasu kuma irin su Cristiano Ronaldo, wanda shi ne ya bude kofar komawa Saudiyya, ana ganin rashin samun babbar kungiya da za ta iya daukarsa ne ya sa ya tafi can domin ci gaba da taka leda.
Wannan ya sa tsohon dan wasan Brazil da Chelsea, Oscar ya ce ya yi farin ciki da a cewarsa yanzu aka fara gane cewa kudi yana da muhimmanci sosai a harkar kwallon kafa.
Oscar yana ganiyarsa a shekarun baya, ya bar Chelsea ya koma China da taka leda bayan an yi sa masa tayin kudi mai yawa, inda a zantarwarsa da manema labarai a lokacin ya bayyana cewa yana bukatar kudi sosai domin daga karamin gida ya fito, kuma yana da nauyi mai yawa a kansa, wanda hakan ya sa yake bukatar kudin.
A lokacin an ta caccakar dan wasan ganin cewa ya bayyana a fili karara cewa kudi ya je nema.
Ga jerin ’yan kwallon da suka koma taka leda a Saudiyya da kuma masu horarwa daga Turai:
Benzema da Neymar da Mane da Mahrez da Firminho dai su ne a gaba bayan Cristiano Ronaldo ya gabace su.
Sauran sun hada da:
.• Kante • Mendy • Saint-Madimin • Gabriel Beiga • Kessie • Bono • Jota • Laporte • Fabinho • Brozović • Aled Telles • Henderson • Ruben • Neves • Koulibaly • Savić • Ibañez • Malcom • Fofana • Mitrović • Demiral • Otávio • Wijnaldum da sauransu.
Masu horas da ’yan wasa • Gerrard • Jorge Jesus • Luis Castro • Matthias Jaissle sai kuma tsohon kocin Italiya, Mancini wanda yanzu shi ne mai horar da kungirar kasar Saudiyya.
Da yake zantawa da Aminiya, wani mai horar da ’yan wasa a Kaduna, Ibrahim Haruna ya ce dama ita kwallo sana’a ce kamar kowace sana’a, inda kowa ke neman riba.
“Yaudarar kai ne a ce ba don kudi ’yan wasan suke tururuwar zuwa Saudiyya ba. To dama ba don kudin ake kwallon ba?
“Yawancin ’yan kwallon nan talakawa ne, suka samu dama suka daga darajar gidansu da kwallon. Babu wanda zai so ya samu dama sannan ya koma baya.
“Shi ya sa suke neman inda za su samu kudi masu yawa. Ko a Turai ma ana haka.
“Za ka matashin dan wasa yana taka leda da kyau, kusan ma za a iya cewa shi ne yake daukar kungiyar da yake, amma da zarar wata kungiya babba ta zo ta sanya masa kudi sosai, sai ya koma can.
“Idan taka ledar kawai yake so, ya tsaya a inda ake matukar son sa mana,” in ji shi.