Fitattun ’yan wasan fim mata 10 daga Kudancin Najeriya (2)
Masana’antar fina-finan Kudancin Najeriya, wadda aka fi sani da Nollywood a takaice, ta kafu tun fiye da shekaru 20 da suka gabata. Ya zuwa wannan lokaci, ta kyankyashe fitattun ’yan wasa da ake ji da su. Idan muka duba jerin gwanon irin wadannan fitattun ’yan wasa daga cikin mata, za mu iya tsinto kamar guda […]

Masana’antar fina-finan Kudancin Najeriya, wadda aka fi sani da Nollywood a takaice, ta kafu tun fiye da shekaru 20 da suka gabata. Ya zuwa wannan lokaci, ta kyankyashe fitattun ’yan wasa da ake ji da su. Idan muka duba jerin gwanon irin wadannan fitattun ’yan wasa daga cikin mata, za mu iya tsinto kamar guda goma a yanzu, wadanda suka fi tashe a wannan lokacin. Wadannan zaratan ’yan mata kuwa, wadanda suka yi fice ta fuskar hazaka da iya wasan fim, mun tsinto su ne domin baje kolinsu a wannan lokaci. A makon jiya ne muka yi nazari kan zababbun matan guda biyar, yanzu kuma ga sauran biyar din:



(6) ’Yar wasa Stephanie Okereke: ’Yar wasa Stephanie, ita ce ta shida a jerin gwanon fitattun mata ’yan fim goma da suka shiga wannan tsari. Ta samu wannan daukaka ne, musamman saboda hazakarta da irin baiwar da Allah Ya yi mata wajen iya fitar da ma’anar
labarin da aka dora ta a kai, a cikin fim. Baya ga wannan baiwa, daraktoci da masu shirya fina-finai suna rububin sanya ta cikin fina-finai ne, a sanadiyyar kyan halitta da ta mallaka. Wadannan dalilai na daga cikin sirrin samun daukakar da ta yi cikin lokaci.
(7) ’Yar wasa Uche Jombo: Wannan ’yar wasa, Uche Jombo, ta kasance diyar da ’yan kallo ke rububin gani, ko dai a zahiri ko kuma a cikin fina-finan da ta fito ciki. Mafi yawan lokaci, ’masu shirya fim a Kudancin Najeriya na yawan ba ta aiki ne saboda amanna da suka yi cewa ta san abin da take yi, idan dai maganar wasan kwaikwayo ne. Wani Furodusa ya taba yin alkawarin cewa, duk fim din da ya shirya, idan dai har Uche ta fito kuma ba ta yi abin gamsarwa ba, to zai mayar wa mai kallo kudinsa. Wannan dalili ne ya sanya ta ciri tuta kuma ta kasance a sahun gaba na fitattun matan fim na Kudancin Najeriya.
(8) ’Yar wasa Kate Henshaw-Nuttal: Ida nana neman ’yar wasan da ke wasa kamar da azazza, mai kallo ya ga kamar gaskiya yake kallo, idan aka samu ’yar wasa Kate, sai a tashi kawai, domin kuwa an samu abin da ake bukata. Duk da cewa tana da barkwanci da raha a zahiri, idan ka sanya ta cikin wasan bata rai, sai ka rantse da Allah cewa ba ta taba yin dariya ba a rayuwarta. Kate, ta kasance ’yar wasa da ke dacewa da kowane irin shiri da aka ba ta. Idan soyayya ce, ta iya. Idan mugunta ce, ta kware. Idan zaman yau da kullum ne na al’umma, za ka same ta cikin dacewa. Dalili ke nan ta yi ta samun kyaututtukan yabawa daga kungiyoyi da hukumomi daban-daban.
(9) ’Yar wasa Ini Edo: Wannan ’yar wasa ta samu shiga cikin wannan tsari, inda ta dauki matsayi na tara. Ta kasance gwana a fagenta na wasan kwaikwayo. Baya ga kyan fuska, ta kuma kasance mai jimiri a wurin daukar fim. Daraktoci ba su cika kuka da ita ba, musamman idan suna kan aiki, saboda yadda take jajircewa. Ta samu nasara ne a sakamakon gamsar da ’yan kallo da take yi a wasanninta.
(10) ’Yar wasa Tonto Dike: Wannan ’yar wasa, ita ce ta kasance ta goma a cikin tsarin fitattu goma na ’yan wasan Kudancin Najeriya. Kamar yadda ta fadi da bakinta, cewa wasannin Rita Dominic ne suka yi mata kaimi har ta shiga harkar fim, ba ta yi ksa a gwiwa ba sai da ta bi dukkan hanyoyin da ita Ritar ta bi, har ta samu daukaka. Wannan ’yar wasa ta kware wajen kawo sauyi a dukkan fim din da ta fito. Ta samu nasara ne a harkar saboda maida hankali ga ayyukanta.