Fitayanu ta nada shugabannin riko a yankin Kudu maso Gabas

kungiyar Agaji ta Fityanul Islam shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya mai hedkwata a Fatakwal  a wani kwarya-kwaryar zamanta da tayi, ranar  Litinin ta yi garambawul , tare da yin wasu sababbin  nade-naden mukamai na  rikon kwarya a kokarin da  kungiyar take yi na kamanta adalci a tsakanin membobinta. Daraktan Agaji na kungiyar Malam Nazir Muhammad […]

Fitayanu ta nada shugabannin riko a yankin Kudu maso Gabas
Fitayanu ta nada shugabannin riko a yankin Kudu maso Gabas

kungiyar Agaji ta Fityanul Islam shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya mai hedkwata a Fatakwal  a wani kwarya-kwaryar zamanta da tayi, ranar  Litinin ta yi garambawul , tare da yin wasu sababbin  nade-naden mukamai na  rikon kwarya a kokarin da  kungiyar take yi na kamanta adalci a tsakanin membobinta. Daraktan Agaji na kungiyar Malam Nazir Muhammad Musa ne ya sanar da haka a hirar su da Aminiya .
Ya ce an bullo da raba mukaman ne domin kowane dan  kungiyar da ke sauran shiyyoyin Kudu maso Gabas su ma su ji ana damawa da su.Wadanda aka nada aikin su taimakawa daraktan shiyyar kudu maso kudu aiki domin ci gaban kungiyar da kuma aikace-aikacenta .
An zabi Jibril Aliyu matsayin sakataren gudanarwa, yayin da Aliyu Suleman matsayin darakta  bayar da horo ga ’yan kungiyarsauran sune Aliyu Muhammad daga Jihar Imo ya zama mai ciken kudi na kungiyar Fityanul-Islam, su kuwa Mustapha Muhammad da Jibril Aliyu masu kula da kayan kungiyar na aiki, sai Bashiru Kabiru matsayin mai ladabtarwa, masu taimakawa kuwa su ne Sani Sa’ad da Zakiru Bello mataimaki na daya da na biyu, Malam Harunan da ke Jihar Bayelsa, sai kuma ya zama mataimakin daraktan shiyya na biyu,  agaji na kungiyar .
A cewar Daraktan agaji Muhammad Musa, za su rike mukaman na wata uku kafin daga bisani a gudanar da zabe.ya yi fatan za su rike amanar da aka ba su su yi aiki tukuru.