Fitowar ’yan takara da yawa kan sa jam’iyya darje wakilai nagari – Dokta Jalo Daudu

Dokta Ibrahim Jalo Daudu shi ne Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe, kuma tsohon Shugaban Ma’aikata na Jihar, fitaccen ma’aikacin gwamnati ne da ya taba zama Babban Sakatare a Ofishin Shugaban kasa da Ma’aikatar Sadarwa ta Tarayya, a tattaunawarsa da Aminiya ya yi tsokaci kan siyasar Gombe da yadda jama’a suke ta kiraye-kirayen ya […]

Fitowar ’yan takara da yawa kan sa jam’iyya darje wakilai nagari – Dokta Jalo Daudu
Fitowar ’yan takara da yawa kan sa jam’iyya darje wakilai nagari – Dokta Jalo Daudu

Dokta Ibrahim Jalo Daudu shi ne Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe, kuma tsohon Shugaban Ma’aikata na Jihar, fitaccen ma’aikacin gwamnati ne da ya taba zama Babban Sakatare a Ofishin Shugaban kasa da Ma’aikatar Sadarwa ta Tarayya, a tattaunawarsa da Aminiya ya yi tsokaci kan siyasar Gombe da yadda jama’a suke ta kiraye-kirayen ya tsaya takarar Sanata a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben 2015:

Aminiya: Kai tsohon ma’aikacin gwamnati ne me ya ba ka sha’awar shiga siyasa?
Dokta Jalo Daudu: Alhamdulillahi kamar yadda aka sani na yi aikin gwamnati daga jiha zuwa tarayya, na yi shekara 32 ina aiki sannan na yi ritaya. Watakila ganin gogewata da kwarewa da ganin gudunmawar da na bayar a baya da kuma kauna ya sa wasu daga cikin al’ummar Gombe ta Arewa suka ce na cancanci in tsaya takarar Sanata.
Aminiya: Wannan yanki na Gombe ta Arewa yanzu haka akwai ’yan takarar Sanata da dama yaya kake ganin nasarar takararka?
Dokta Jalo Daudu: To har yanzu, ban yanke hukuncin zan tsaya din ba tukuna, amma dai yana da kyau a samu masu tsayawa takara fiye da mutum guda ko biyu. Wannan zai ba jama’a da ita jami’iyya ta zabi mafi cancanta da karbuwa don samun wakilci mai inganci.
Aminiya: Ka taba shiga harkar siyasa ce a baya?
Dokta Jalo Daudu: Eh, a shekarun baya na yi siyasa har ma na yi takarar dan Majalisar Tarayya, a wancan lokaci Allah bai ba ni nasara ba. Daga bisani na ci gaba da aikin gwamnati sai kuma yanzu bayan na yi ritaya shi ne na shiga Jam’iyyar PDP saboda na ga tana da manufofi kyawawa na ci gaba. Kuma za ta ba ni damar taimaka wa Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo, wajen ciyar da Jihar Gombe gaba, ba kuma lallai don samun wata kujera ba. Ina shirye na ba da gudunmawa don ci gaban al’umma da kasa a kowane lokaci. A yanzu haka mai girma Gwamna ya ba ni shugabancin sabuwar hukumar nan ta lafiya wato Primary Health Debelopment Agency, kuma babbar dama ce ta ci gaba da ba da gudunmawa ga al’ummar Gombe.
Aminiya: Mutanen Jihar Gombe na korafin cewa babu walwala a zamanin Gwamna dankwabo, duk da sun yarda ana aiki, me za ka ce?
Dokta Jalo Daudu: Gaskiya Gwamna dankwambo na aiki ba kama hannun yaro, amma cewa jama’a na korafin rashin walwala ban ji ba. Saboda idan ka lura a shekara uku da rabi na mulkin Gwamna dankwambo, Jihar Gombe ta yi wa takwarorinta fintinku, kuma duk ayyukan ci gaba da dankwambo yake gudanarwa masu inganci ne da tsari. Dubi hanyoyin zamani a birni da karkara, ga makarantun firamare duk benaye aka gina, ga asibitoci komai ya inganta, to me ake nema kuma? Idan aka lura wannan Gwamna namu yana da kishin jiharsa ba abin da yake nema yanzu illa jama’ar Gombe su kara ba shi haddin kai da cikakken goyon baya a zaben da ke tafe a badi, saboda ya ci gaba da samar mana da abubuwan more rayuwa. Batun ana korafin rashin walwala, na san jama’ar Gombe ’yan kasuwa ne ko masu sana’o’I, ba su dogara kacokan a kan gwamnati ba. Tun fil azal idan gari ya waye gani za ka yi mutane na ta kokarin tafiya kasuwanni na cikin gari da na kauyuka don saye da sayarwa ko wuraren sana’o’insu da damina kuma su nufi gonakinsu, ashe ba wani korafi da za a ji. Sai dai mu roki Gwamnan ya kara inganta mana harkokin kasuwancin da bangaren noman rani da na damina saboda wadata jiharmu da abinci. Kamar yadda na fada a baya babu abin da jama’ar za su yi wa Gwamnan illa su ci gaba da yi masa addu’a da kuma sake ba shi goyon baya, duk abin da gwamnati za ta yi, sai ta samu hadin kai da goyon bayan al’umma sannan kome ya tafi daidai. Hakika kowannenmu yana da gudunmawar da zai bayar don raya kasa tamkar daukar jinka ne.
Aminiya: Ka ce gwamnatin dankwambo, tana ayyukan raya kasa, yaya walwalar ma’aikata fa?
Dokta Jalo Daudu: A Gombe babu watan da ake tsallakewa ba a biya albashi ba, saboda Gwamna dankwambo gogaggen ma’aikacin gwamnati ne kafin ya shiga siyasa, shi ya sa ya dauki ma’aikata da muhimmanci domin su ne kashin bayan gwamnati. A yanzu haka ya ba da aikin gina babbar sakatariyar jiha, kuma an kusan kammalawa, kuma akwai fiye da ma’aikatan gwamnati 1500 da yanzu ake ba su horon sanin makamar aiki da aka fara fiye da mako biyu, bayan sun gama za a sake dauko wasu har sai kowanne ma’aikaci a jihar ya samu horo. Ina kira ga jama’a gaba daya su kara hakuri don manyan ayyukkan da ake yi, duk alheri ne kuma kaka mai dimbin albarka za ta biyo baya.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya