Fitsari da kashin zomo na samar wa makiyaya Naira dubu 100 a wata — NALDA

Hukumar Bunkasa Harkar Noma ta Kasa (NALDA) ta fito da wani shiri kan masu kiwon zomo, inda hukumar ta dauki masu kiwon zomo dubu 17 daga Kudancin Najeriya, wadanda za ta raba musu zomaye dubu biyar a jihohin Imo da Abiya da Kurosriba da Oyo a kashin farko na shirin. Matasan da shirin ya dauka […]

Fitsari da kashin zomo na samar wa makiyaya Naira dubu 100 a wata — NALDA

Zomaye

Hukumar Bunkasa Harkar Noma ta Kasa (NALDA) ta fito da wani shiri kan masu kiwon zomo, inda hukumar ta dauki masu kiwon zomo dubu 17 daga Kudancin Najeriya, wadanda za ta raba musu zomaye dubu biyar a jihohin Imo da Abiya da Kurosriba da Oyo a kashin farko na shirin.

Matasan da shirin ya dauka domin koya musu kiwon tuni suka fara samun kudi daga kiwon inda akalla suke samun kimanin Naira dubu 100 daga kashi da fitsarin zomayen da suke sayarwa duk wata.

Babban Sakatare kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na NALDA, Prince Paul Ikonne, shi ne ya bayyana hakan a Abuja a lokacin da yake zantawa da manema labarai inda ya ce shirin sabo ne da yake kunshe da albarkatu masu yawa.

Ya ce hukumar tuni ta fara gudanar da kashi na farko a bangaren kula da dabbobi tare da karfafawa a kan awaki da zomaye wanda Shugaban Kasa ya bada dama domin daukar matasa kimanin dubu 774 a bangaren aikin gona da kasuwancinsa a fadin qasar nan.

A cewarsa, daga ranar farko da aka fara kiwon zomo mutum zai fara samun kudi daga tattara kashi da fitsarinsu wanda ake amfani da su a matsayin taki a gonaki kuma kudin da zai samu suna ci gaba da karuwa.