Fiye da mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Katsina

Babu abin da muka gani a mulkin APC sai rashin adalci, fatara, yunwa, garkuwa da mutane da kashe-kashe.

Fiye da mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Katsina

A ranar Asabar ce jam’iyyar adawa ta PDP ta karbi wani jigo tare da dubban magoya bayansa da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Katsina.

Jigon jam’iyyar APC, Alhaji Ali Maikano Matazu, wanda tsohon darakta ne a Kamfanin Man Fetur na  Najeriya (NNPC), ya tsaya takarar dan Majalisar Wakilai a mazabar Matazu/Musawa ta tarayya amma ya sha kaye, inda ya kira lamarin a matsayin “zaluncin jam’iyyar”.

Bayanai sun ce, wadanda suka sauya shekar sun samu tarba daga dan takarar gwamnan jihar na PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke tare da shugaban jam’iyyar na jihar, Yusuf Salisu Majigiri da sauran shugabannin jam’iyyar a Matazu.

Da yake zantawa da wakilinmu, shugaban jam’iyyar na jihar, Majigiri, ya ce sama da mambobin jam’iyyar APC 5,000 ne suka sauya sheka zuwa PDP a yayin taron.

A jawabin da ya yi ga dimbin jama’ar da suka taru a garin Matazu, Sanata Danmarke ya yi ikirarin cewa, jam’iyyarsu ce ta lashe dukkan kujerun kananan hukumomin a zaben da aka gudanar kwanan nan, amma jam’iyyar APC mai mulki ta yi musu babakere.

Yadda jama’a suka halarci taron sauyin shekar a Katsina

Sai dai ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa a zabe mai zuwa, jam’iyyar PDP za ta samu nasara a jihar cikin sauki, yana mai cewa matukar Hukumar Zabe ta kasa ta gudanar da zaben gaskiya babu shakka za a yi nasara.

Kazalika, Sanata Danmarke ya bukaci daukacin yan jamiyyar da magoya bayansa da su tabbatar sun mallaki katin zabe wanda shi ne makaminsu na zabar shugabanni na gari.

A nasa jawabin, Alhaji Ali Maikano, wanda aka bai wa dan takarar jam’iyyar PDP na mazabar Matazu, kasancewarsu a jam’iyyar APC, babu abin da suka gani sai rashin adalci, fatara, yunwa, garkuwa da mutane da kashe-kashe.

Ya ce wannan dalili ya sanya suka yanke shawarar dawowa PDP don ceto jihar daga halin da tsinci kanta a yanzu.

A jawabin da ya yi tun a karon fari, shugaban jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Matazu, Jabiru Adamu Rinjin Idi, ya ce, PDP reshen Karamar Hukumar Matazu ce ta farko da ta karbi ’yan jam’iyyar da suka sauya sheka daga wasu jam’iyyu da daban-daban tun bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyu, inda ya ce yana fatan sauran kananan hukumomin za su yi koyi da hakan.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu