Fiye da mata 60 suka samu horo a wa’adinmu na farko –Shugabar NAWOJ

Shugabar Kungiyar Mata ’Yan Jarida ta Kasa (NAWOJ), reshen Jihar Gombe, Misis Comfort Mukollo ta ce fiye da mata ’yan jarida 60 ne a jihar suka samu horo a bangarorin aikin jarida a shekara uku na shugabancinta karo na farko. Misis Comfort Mukollo, ta bayyana haka ne jim kadan da rantsar da ita a karo […]

Fiye da mata 60 suka samu horo a wa’adinmu na farko –Shugabar NAWOJ

Shugabar Kungiyar Mata ’Yan Jarida ta Kasa (NAWOJ), reshen Jihar Gombe, Misis Comfort Mukollo ta ce fiye da mata ’yan jarida 60 ne a jihar suka samu horo a bangarorin aikin jarida a shekara uku na shugabancinta karo na farko.

Misis Comfort Mukollo, ta bayyana haka ne jim kadan da rantsar da ita a karo na biyu bayan ta sake lashe zaben shugabar kungiyar na wasu shekara uku.

Ta  ce, mata ’yan jarida su shirya don za su sake cin ribar wasu horarwa kamar yadda ta yi a baya don ganin mata ’yan jarida suna gogayayya da takwarorinsu maza ba a Jihar Gombe kadai ba a fadin kasar nan.

Ta yi alkawarin ci gaba da  tafiyar da adalci tare da  ciro wa ’ya’ya kungiyar kitse a wuta.

Comfort Mukollo, wadda take aiki da gidan talabijin din Jihar  Gombe (GMTB), an sake zabar ta ce ba tare da hamayya ba. Sauran wadanda aka zaba sun hada da Talatu Lamon daga NTA a matsayin Mataimakiyar Shugaba sai Salome Mohammed daga Ma’aikatar Watsa Labarai, a matsayin  Sakatariya.

Sauran sun hada da Malama Hafsat Hamza daga gidan Rediyon Gombe a matsayin Ma’aji, sai Hauwa Jijji, Sakatariyar Kudi daga Ma’aikatar Watsa Labarai, sai kuma Balkisu Bibi Lakuto, Mataimakiyar Sakatariya daga GMTB, sai Jummai Maigari Lakata Mai Binciken Kudi.