‘Fiye da mutane dubu 30 suke sayar da doya a Jihar Bauchi’

Alhaji Rilwanu Ibrahim Katsinawa shi ne Shugaban kungiyar masu sayar da doya na Jihar Bauchi, a cikin tattaunawarsa da wakilinmu ya yi bayani game da gudunmuwar da ’yan doya suke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Za mu fara da gabatar da kanka? Sunana Alhaji Rulwanu Ibrahim Katsinawa, shugaban kungiyar […]

‘Fiye da mutane dubu 30 suke sayar da doya a Jihar Bauchi’
‘Fiye da mutane dubu 30 suke sayar da doya a Jihar Bauchi’

Alhaji Rilwanu Ibrahim Katsinawa shi ne Shugaban kungiyar masu sayar da doya na Jihar Bauchi, a cikin tattaunawarsa da wakilinmu ya yi bayani game da gudunmuwar da ’yan doya suke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu fara da gabatar da kanka?

Sunana Alhaji Rulwanu Ibrahim Katsinawa, shugaban kungiyar masu sayar da doya na kasa reshen Jihar Bauchi. kungiyar ’yan doya tana daya daga cikin tsofaffin kungiyoyi a Najeriya, kuma muna bada gagarumar gudunmawa wajen samar wa matasa aikin yi, domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani sai matasa sun zamo masu dogoro da kai. Sama da shekara 25 zuwa 30 wannan kungiya tana bada gudunmawa a Najeriya. A wannan kasuwa akwai masu saye da sayarwa; akwai dillalan doya; akwai ’yan dako da kuma masu dauka da saukewa, ka ga kuwa muna taimakawa sosai wajen dakile zaman kashe wando a tsakanin al’umma.Tun lokacin da aka kafa wannan kungiya a Bauchi an yi shugabannin kusan 10.
Wadanne matsaloli kuke fuskanta a halin yanzu?
kungiyarmu ta fuskanci matsaloli iri-iri, misali akwai lokacin da aka tsare motarmu ta ’yan doya a yankin karamar Hukumar Tafawa-balewa a Jihar Bauchi, inda aka kashe mutane biyar. Mun kai rahoto ga hukumomin tsaro, amma har zuwa wannan lokaci babu wani mataki da aka dauka a kan wadanda suka aikata kisan. Babu wata gudunmawa da muka samu daga gwamnati. Gwamnatin Isa Yuguda ta dabe mana cikin kasuwarmu har da kasuwar ’yan gwari shekarun baya, amma zuwa yanzu babu wani taimako da muka sake samu.
Wadanne nasarori ka samu dalilin sana’ar sayar da doya?
Ina alfahari da wannan sana’a dari bisa dari, domin na yi gida, na yi aure, sannan ina tallafa wa dimbin mutane ta sanadiyyar sana’ar. Ina so ka fahimci cewa duk wanda ya saba da wannan sana’a ba zai iya aikin gwamnati ba, domin aikin gwamnati sai wata, doya kuma ta kullum ce. ko ka saya, ko kuma ka sayar.
Mambobin wannan kungiya sun kai mutum nawa a Bauchi?
A Jihar Bauchi muna da mambobi sama da mutum dubu 30, ko fiye da haka, kuma dukkansu babu abin da suka sani a rayuwa sai sana’ar doya, bayan haka akwai dimbin matasa wadanda kullum a nan kasuwar suke samun kudin sayan abinci, wasu sun gina gidaje, wasu sun je aikin hajji. Kullum sai an sauke motar doya sama da 20 a nan Bauchi, kuma duk motar da aka sauke doya karamar hukuma tana samun kudin shiga.
Yaya dokokin kungiyarku suke?
Dokokin kungiyar su ne, ba ma yi wa mutum rijista sai ya kawo mana wanda muka amince da shi, domin idan ya yi wani abu mun san inda za mu same shi.
Me za ka ce game da batun Tabita Haruna wadda aka ce an kashe ta a kofar kasuwarku ta ’yan doya?
Farko muna mika sakon ta’aziyyarmu ga mahaifiyarta da sauran ’yan uwanta bisa abin da ya faru. Gaskiyar magana ita ce ba a kashe Tabita Haruna a kofar kasuwar ’yan doya ba, kuma babu wani daga cikin mambobinmu da aka kama bisa wannan aika-aika. Wadanda suka sa mata taya suka kona ta ba mu san daga ina suka fito ba. Domin kowa ya san cewa mu mutane ne masu bin doka da oda, kuma mutanenmu masu yi wa shugabanni biyayya daidai bakin gwargwado ne.
Daga karshe mene ne sakonka ga al’umma?
Babban sakona ga al’umma shi ne, don Allah mu ci gaba da zama lafiya, domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba sai da zaman lafiya. Ina kira ga mambobinmu su ci gaba da bin doka da oda a duk inda suka samu kansu.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu