Fiye da mutum 13,000 sun kamu da Kwalara a Borno

Rahoton Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa cutar Kwalara ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 17 daga cikin 27 da ke Jihar Borno.

Fiye da mutum 13,000 sun kamu da Kwalara a Borno

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar Kwalara a Jihar Borno ya kai 108, yayin da aka samu sama da mutum 13,000 da suka kamu da cutar tun daga farkon watan Mayun 2026.

Rahoton Ma’aikatar Lafiya da Kula da Lafiyar Jama’a ta Jihar Borno ya nuna cewa an samu mutum 13,234 da suka kamu da cutar a faɗin jihar zuwa ranar 18 ga watan Yuni.

Daga cikin mace-macen da aka samu, 71 sun faru ne a cibiyoyin lafiya, yayin da 37 suka mutu a cikin al’umma kafin samun kulawar likitoci.

Rahoton ya nuna cewa cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 17 daga cikin 27 da ke jihar.

Birnin Maiduguri ne ya fi yawan masu kamuwa da cutar da mutum 7,083, sai Jere da mutum 3,403, yayin da Konduga da Monguno suma ke cikin yankunan da suka fi fama da annobar.

A ranar 18 ga watan Yuni kaɗai, an samu sabbin masu kamuwa da cutar 236, yayin da mutum 226 suka kwanta jinya.