Fiye da mutum 300 ne cutar Ebola ta kashe a Yammacin Afirka
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar Ebola a yankin Yammacin Afirka ya karu zuwa 337.Hukumar ta cewa a makon jiya kadai an samu rahotan mutuwar mutum 47 da kuma bullar cutar a wasu yankuna.kasar Guinea ce dai annobar Ebola ta fi addaba, inda a can […]
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar Ebola a yankin Yammacin Afirka ya karu zuwa 337.
Hukumar ta cewa a makon jiya kadai an samu rahotan mutuwar mutum 47 da kuma bullar cutar a wasu yankuna.
kasar Guinea ce dai annobar Ebola ta fi addaba, inda a can aka tabbatar da mutuwar mutum 264 sanadiyyar harbuwa da kwayar cutar. Hakazalika a kasar Sierra Leone mutum 49 ne suka mutu, a Liberiya kuma mutum 24. kasashen uku sun fara yaki da cutar ne tun a watan Fabrairun bana.
Wani mutum Firmin Bogon wanda ya rasa ’yan uwansa 10 sanadiyyar annobar da ke zaune a garin Gueckedou na kan iyakar Liberiya da Sierra Leone. Ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa ya rasa yayarsa da mai dakinsa da kishiyar mahaifiyarsa da kuma sauran ’yan uwansa duk ta sanadiyyar annobar.
Jemage ne dai babban mai yada cutar. A wani mataki na takaita yaduwar annobar, a kasar Guinea, hukumoni sun haramta sayar da jemage, da kuma cin namansa duk da cewa yana daya daga cikin abincin wasu daga cikin mutanen kasar.