Fiye da mutum miliyan 1 ne Masallacin Manzon Allah zai dauka bayan fadada shi

Masallata miliyan daya da dubu 600 ne Masallacin Manzon Allah da ke birnin Madinah zai dauka bayan an kammala aikin fadada shi. Fiye da ma’aikata dubu biyar ne ke aiki ba dare, ba rana domin kammala aikin fadada masallacin da ba a taba gani ba a tarihi. Har ila yau, fiye da kashi 95 cikin […]

Fiye da mutum miliyan 1 ne Masallacin Manzon Allah zai dauka bayan fadada shi
Fiye da mutum miliyan 1 ne Masallacin Manzon Allah zai dauka bayan fadada shi

Masallata miliyan daya da dubu 600 ne Masallacin Manzon Allah da ke birnin Madinah zai dauka bayan an kammala aikin fadada shi.

Fiye da ma’aikata dubu biyar ne ke aiki ba dare, ba rana domin kammala aikin fadada masallacin da ba a taba gani ba a tarihi. Har ila yau, fiye da kashi 95 cikin 100 na rushe-rushen bangarorin da za a fadada an rigaya an kammala. Kuma akalla otel 10 ne aka rushe da ke gabashin masallacin da wasu gidajen masu dama domin ci gaba da aikin fadada masallacin mai alfarma.
Daraktan Hulda da Jama’a kan masallacin Abdul Wahid bin Ali ya ce idan aka kammala zangon farko na aikin, masallacin zai dauki mutane dubu 800. Yayin da bayan kammala fadada bangaren gabashi da yammacin masallacin shi ma zai dauki wasu masallata dubu 800. “Ka ga ke nan idan aka kammala aikin gaba daya, masallacin zai kunshi mutane miliyan daya da dubu 600 a lokaci guda,” inji shi. Daraktan ya kara da cewa masallacin a yanzu yana daukar masallata dubu 600.
Har ila yau, Daraktan Ma’aikatar Aikin Hajji reshen birnin Madinah, Muhammad al- Bijawi ya ce rushe-rushen da aka yi bai shafi baki mazauna kasar ba, saboda matakan da aka dauka tun farko domin kiyaye hakan.