FOMWAN ta fadakar da mata muhimmancin hijabi a Yobe
Shugabar kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen Jihar Yobe, Hajiya Hauwa Buba ta ce kungiyarsu ta dukufa wajen ilmantar da mata muhimmancin hijabi. Shugabar ta bayyana hakan ne a jawabinta wajen bikin ranar sa Hijabi ta duniya da aka gudanar a Masallacin Juma’a da ke cibiyar kula da addinin Musulunci da ke garin Damaturu […]
Shugabar kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen Jihar Yobe, Hajiya Hauwa Buba ta ce kungiyarsu ta dukufa wajen ilmantar da mata muhimmancin hijabi.
Shugabar ta bayyana hakan ne a jawabinta wajen bikin ranar sa Hijabi ta duniya da aka gudanar a Masallacin Juma’a da ke cibiyar kula da addinin Musulunci da ke garin Damaturu a Jihar Yobe.
Ta ce ranar sa Hijabi ta duniya na da matukar muhimmanci, domin Hijabi sutura ne da ke kare tsiraicin ’ya’ya mata, kasancewar addinin Musulunci ya tanadar da cewar duk mace tagari ta kan sa Hijabi ne daga kanta har kasa da nufin kare mata mutunci tare da kauce wa nuna surarta da zai sa har maza su nuna sha’awa gare ta a fili, inda a karshe hakan kan taimaka wajen jawo hankalin bata garin mutanen da ke aikata mummunan halayyar nan ta fyade.
Amirar ta kawo takaitaccen tarihin samuwar wannan rana ta sa Hijabi ta duniya da cewar, wata ’yar uwa ce a kasar Amurka Nazma Khan ta kirkiro wannan rana shekara 2 da ta gabata, kuma saboda muhimmancin hakan ne ya sa ba tare da bata lokaci ba aka samu kimanin kasashe 67 ciki har da Najeriya ke gudanar da bikin a ranar 1 ga Fabarairu ta kowace shekara.
Ta bukaci iyaye mata Musulmi a ko’ina suke su rika sa Hijabi tare da umartar ’ya’yansu mata su rika sawa.
“Itace tun yana danye ake tankwasa shi, don haka sai sun koya wa ’yayansu sanya hijabi kafin su taso da hakan. Alhamdulillahi, a yanzu idan aka duba ’ya’ya mata a birni da kauye za ka tarar akasarinsu sanye suke da Hijabi.” Inji ta.
Sakataren dindindin na Ma’aikatar Kula da addini ta Jihar Yobe Alhaji Bukar Madu Jimbam ya bukaci mata su yi amfani da abin da suka saurara yayin taron.
Da ya ke nasiha a wajen wannan bikin daya daga cikin malaman da aka gayyato Malam Mustafa Ibrahim ya kawo ayoyi ne daga cikin Alkur’ani mai girma da kuma hadisan Manzon Allah SAW da suke horo da sa hijabi da irin muhimmancinsa ga ’ya’ya mata.
Ya ce: “Shiga ta mutunci kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, to dole ne a suturta dukkan jikin ’ya’ya mata daga sama har kasa tare da guje wa tafiya irin ta jiji-da-kai kamar yadda matan kafiran farko suke yi.”
Malam Ahmad Adamu a cikin fadakarwarsa cewa ya yi, masana irinsu Dr Muhammad Auwal Ahmad sun ce sa Hijabi kan kara musu lafiyar jiki ta yadda hijabin kan kare fatar jikinsu daga kamuwa da cutukan fata.
“Hijabi kan kare mata daga kamuwa daga shafar aljannu tare da kara musu laushin fatar jiki da sauran abubuwan alhairai.”
Kungiyar ta rarraba kayayyakin abinci ga mutane kimanin 100 da suke gudun hijira. Kayayyakin sun hada da buhun shinkafa 20 da na wake 7 da magi katan 5 da man girki jarka 10. Ta raba kayayyakin ne ga magidantan da suka yi gudun hijira daga garuruwan Gujba da Gulani da Goneri da Gwoza da Chibok da sauransu.