Fostar fim din Zindagi Na Milegi Dobara
Daga dukkan alamu, a azumin bana ba za a samu kamfar sabbin fina-finai ba a masana’antar fina-finan Indiya da aka fi sani da Bollywood ba; kamar yadda mujallar Hindustan Times ta ruwaito.A kowane watan azumi, harkokin fina-finai kan tsaya cik a Indiya, inda mafi yawan ’yan wasa kan huta ko kuma su fuskanci wasu al’amuran […]


Daga dukkan alamu, a azumin bana ba za a samu kamfar sabbin fina-finai ba a masana’antar fina-finan Indiya da aka fi sani da Bollywood ba; kamar yadda mujallar Hindustan Times ta ruwaito.
A kowane watan azumi, harkokin fina-finai kan tsaya cik a Indiya, inda mafi yawan ’yan wasa kan huta ko kuma su fuskanci wasu al’amuran na gaban kansu. A bana an samu tabbacin cewa za a samu fitowar sababbin fina-finai.
“Ba na tsammanin a bana za a samu kamfar sababbin fina-finai a Bollywood,” inji Taran Adarsh, wani mai sharhi kan al’amuran kasuwancin fina-finai a Indiya. “Na farko dai masana’antar fina-finan Indiya tana fuskantar wani sauyi, ko kuma in ce juyin-juya-hali; musamman tun da aka fitar da manyan fina-finan Ready, Double Dhamaal zuwa Delhi Belly, Murder 2, ga kuma yanzu da aka fitar da Zindagi Na Milegi Dobara a kasuwa. Haka ake ci gaba ruwan manyan fina-finai ba kaukautawa. Wannan kuwa al’amari ne mai faranta rai da kuma ban mamaki a bana, domin kuwa a baya an saba da faduwar kasuwa a watan azumi da ragewar fitowar sabbin fina-finai.”
Haka kuma ana sa ran kasuwar fina-finan tare da fitowar su za ta habaka a watan Agustan bana. Kamar yadda wani masanin kasuwancin fina-finai, Komal Nahata ya ce: “Dubban masu kallon fina-finai suna taimaka wa kasuwancin fina-finai kuma ga shi al’umar Musulmi kan yawaita kallon fina-finai a wannan lokaci.”
A lokacin da fim din Ajay Debgn mai suna Singham ya haddasa cikar gidajen silima da yawa, a yanzu kuma an zuba ido ga fitowar babban fim din Aaraksham, wanda a cikinsa ne manya da kuma shahararrun taurari masu tashe kamar su Saif Ali Khan da Amitabh Bachchan da Deepika Padukone suka taka rawa. Ana sa ran fitar fim din a ranar 12 ga Agustan bana.
Wani rahoto kuma ya tabbatar da cewa fim din Salman Khan mai taken Bodyguard zai fita daidai lokacin Idin karamar Sallah.
“Ke nan masu bukatar kallon sabbin fina-finai ba za su gamu da haushi ba, ganin cewa al’amura a azumin bana sun canza.” Inji wani mai mai kwakwar kallon fina-finai a Indiya.