FRSC ta bukaci direbobi su rika tsare ka’idojin tuki
Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC), shiyyar dambatta ta bukaci direbobi da masu abin hawa su rika aiki da dokokin tuki domin kauce wa aukuwar haddura a kan hanyoyi. Kwamandan Shiyyar Alhaji G. I. Tsoho ne ya bayyana haka ta bakin kakakin hukumar Malam Abdullahi Adamu Muhammed Yalwa bayan kammala wani gangamin wayar da kan […]
Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC), shiyyar dambatta ta bukaci direbobi da masu abin hawa su rika aiki da dokokin tuki domin kauce wa aukuwar haddura a kan hanyoyi. Kwamandan Shiyyar Alhaji G. I. Tsoho ne ya bayyana haka ta bakin kakakin hukumar Malam Abdullahi Adamu Muhammed Yalwa bayan kammala wani gangamin wayar da kan direbobi da aka gudanar a makon jiya. Malam Abdullahi Yalwa ya ce hukumar tana kokarin ilimantar da direbobi da fasinjoji da masu abin hawa kan bin ka’idojin hanya, kuma a cewarsa haddura suna raguwa saboda fadakarwar da hukumar ke yi. Shugaban ya danganta wasu haddura da ake samu kan tukin ganganci da daukar kaya ko mutanen da suka wuce ka’ida a cikin mota. Malam Abdullahi Yalwa ya bukaci direbobi su kara kokarin sanin dokokin tuki da kauce wa daukar kayan da ya wuce ka’ida domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya ce jami’an hukumar za su ci gaba da hukunta duk direban da ya karya dokokin tuki. kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen tashar motar Badume ta bakin Saja Dawaye Badume ta nuna jin dadi bisa yadda jami’an hukumar FRSC shiyyar dambatta suke shirya gangami a kai-a kai domin wayar da kan direbobin. Wasu daga cikin direbobin da suka zanta da Aminiya a karshen taron, sun yaba wa hukumar bisa kokarin da take yi na fadakar da su kan dokokin tuki, sun ce hakan yana taimakawa wajen rage haddura, kuma za su hada hannu da hukumar wajen kare rayuka da lafiya da kuma dukiyoyin al’umma.